Duniya

New Zealand Ta Fara Yakin Neman Zabe Bayan Rushe Majalisar Dokoki.

An rushe Majalisar Dokoki ta 54 na New Zealand a hukumance ranar Alhamis, 1 ga Oktoba, lamarin da ke nuna ƙarshen wa’adin majalisar da kuma fara tsarin da zai kai ga babban zaɓen ranar 7 ga Nuwamba.

An ɗauki wannan matakin rushewa ne bayan zaman ƙarshe na majalisar a ranar 23 ga Satumba, wanda ya kawo ƙarshen wa’adin shekaru uku na majalisar da ya fara bayan zaɓen Oktoba na 2023.

Ana sa ran Gwamna-Janar zai fitar da takardar umarnin gudanar da zaɓen a ranar 4 ga Oktoba, inda zai umurci Hukumar Zaɓe a hukumance ta gudanar da zaɓen.

KARANTA KUMA: New Zealand na son Amurka ta ƙara shiga harkokin yankin Pacific

Za a gudanar da zaɓen ne bisa tsarin zaɓe na New Zealand mai suna ‘Mixed Member Proportional’ (MMP), inda masu zaɓe ke kaɗa kuri’a ga ɗan takarar yankinsu da kuma jam’iyyar siyasa.

Jam’iyyar National Party mai mulki, wadda Firayim Minista Christopher Luxon ke jagoranta, tana cikin haɗin gwiwa da jam’iyyun ACT New Zealand da New Zealand First.

Jam’iyyar adawa ta Labour Party ita ma tana neman kafa gwamnati mai zuwa, inda ake sa ran yakin neman zaɓen zai mayar da hankali kan batutuwa da suka haɗa da tsadar rayuwa, tafiyar da tattalin arziki, da ayyukan gwamnati.

Tsarin MMP na New Zealand galibi yana haifar da haɗin gwiwa ko yarjejeniyar samun goyon baya tsakanin jam’iyyu, lamarin da ke bai wa ƙananan jam’iyyu muhimmiyar rawa wajen tantance yadda gwamnati za ta kasance.

An tsara gudanar da babban zaɓen na 2026 a ranar Asabar, 7 ga Nuwamba, inda za a buɗe rumfunan zaɓe daga karfe 9 na safe zuwa 7 na yamma a ranar zaɓen.

An tsara fara kaɗa kuri’a daga ƙasashen waje a ranar 21 ga Oktoba, yayin da za a fara karɓar kuri’u tun kafin ranar zaɓen (advance voting) a New Zealand a ranar 26 ga Oktoba mai zuwa.

An tsara Hukumar Zaɓe za ta sanar da sakamakon zaɓen a hukumance a ranar 27 ga Nuwamba.

 

Reuters/Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button