Shugaban Taiwan Ya Ce Tsibirin zai kare ‘yanci Tare Da Daraja Zaman Lafiya.

Shugaban Taiwan Lai Ching-te ya bayyana cewa suna daraja zaman lafiya amma ba za su yi watsi da ‘yancinsu ba dole ne a mutunta haƙƙin al’ummar Taiwan na ci gaba da kasancewa a matsayin kasa mai cin gashin kanta.
An bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin jawabin bikin Ranar Ƙasa a Taiwan.
Rahotanni sun nuna cewa Taiwan wadda ke tafiyar da harkokinta ta hanyar dimokuradiyya na fuskantar karuwar matsin lamba na soja da siyasa daga Chana wadda ke kallon tsibirin a matsayin wani bangare na yankinta duk da tsananin adawar gwamnatin Taipei.
Sojojin Chana na kara sabbin makamai na zamani kamar jiragen yaki masu boye kansu daga radar (stealth-fighter jets) jiragen ruwa masu daukar jiragen sama da tarin makamai masu linzami yayin da Taiwan ke kara kashe kudi wajen tsaro da kuma zamantar da rundunarta ta soja.
Lai ya ce zaman lafiya ba zai iya dogaro kawai kan “buri” ba Taiwan na daraja zaman lafiya amma ba za mu yi watsi da ‘yancinmu ba. “Muna maraba da tattaunawa da mu’amala amma ba za mu amince da zama a karkashin ikon wani ba.”
Ya kara da cewa kudurin Taiwan ba wai kawai batun tsira ne a yayin da ake fuskantar “fadada ikon gwamnatocin kama-karya” ba.
“Batun ya shafi ko al’ummar duniya har yanzu sun yi imani cewa karfin soja ba zai iya karya dokoki ba kuma cewa masu karfi ba za su iya kwace haƙƙin al’umma na yanke hukunci kan makomarsu ba.”
KARANTA KUMA: Taiwan Ta Gudanar Da Atisayen Yaki Na Hadin Gwiwa Na Farko Ta Amfani Da Jiragen Sama Marasa Matuki (drones)
Amurka ce babbar mai goyon bayan Taiwan a duniya duk da rashin cikakken huldar diflomasiyya a hukumance.
“Kuma muna karfafa karfinmu na kare kanmu ba don mu yi watsi da tattaunawa ba sai dai don tabbatar da cewa tattaunawar za ta iya gudana cikin mutunta juna da daidaito” in ji shi yayin jawabi ga taron.
Ya kara da cewa “Dole ne a mutunta haƙƙin al’ummar Taiwan na ci gaba da kasancewa.”
A shekarar 2024 jim kadan bayan jawabin Lai na farko na Ranar Ƙasa a matsayin shugaba Chana ta gudanar da atisayen soja a kusa da tsibirin abin da ba ta yi ba a shekarar da ta gabata.
Atisayen soja na karshe da ta yi kusa da Taiwan ya faru ne a karshen watan Disamba bayan labarin yarjejeniyar sayen makamai tsakanin Amurka da Taipei na dala biliyan 11 wanda shi ne mafi girma a tarihi.
Shugaban Amurka Donald Trump bai riga ya amince da karin kunshin sayen makamai na dala biliyan 14 ba.
Lai ya ce yana maraba da yadda Amurka da Chana ke tafiyar da gasar da ke tsakaninsu ta hanyar tattaunawa da kuma rage barazanar rikici da yaki. Ya yi kira ga kasashen da ke tafiyar da tsarin dimokuradiyya a yankin Indo-Pacific da su hada karfi da karfe domin kiyaye yanayin zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.
Ana gudanar da bikin Ranar Kasa ta Taiwan ne domin tunawa da tawayen shekarar 1911 wanda ya kai ga kawar da daular sarakuna ta karshe a kasar Sin tare da kafa Jamhuriyar Sin.
Gwamnatin jamhuriyar ta tsere zuwa Taiwan a shekarar 1949 bayan ta sha kashi a yakin basasa da suka yi da ‘yan gurguzu karkashin jagorancin Mao Zedong kuma Jamhuriyar Sin ce har yanzu sunan hukuma na tsibirin.



