Majalisar Dokoki Ta Kasa Ta Ci Gaba Da Zaman Majalisa Bayan Hutun Shekara-Shekara

Majalisar Dokokin Najeriya ta koma zamanta na yau, Talata, 29 ga Satumba, bayan hutun shekara-shekara.
Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai za su koma kan harkokin majalisa bayan tsawaita hutun, wanda aka tsara zai ƙare a farkon wannan watan.
Ana sa ran ‘yan majalisa za su mayar da hankali kan harkokin majalisa da ke jiran a yi, ciki har da gyare-gyaren kundin tsarin mulki, gyare-gyaren zabe da kuma kula da aiwatar da kasafin kudin kasa na 2026.
KARANTA KUMA: Yaƙin neman zaɓe na 2027 Ba Zai Shafi Ayyukan Majalisa ba — Shugaban Majalisar Dattawa
Ana kuma sa ran tsarin gyaran kundin tsarin mulki zai ci gaba da zama babban batu bayan mika shawarwarin gyare-gyare ga Majalisar Dokokin Jihohi 36 don nazari.
Gyare-gyaren da aka gabatar sun shafi batutuwa da suka hada da ‘yan sandan jiha, gudanar da kananan hukumomi, batutuwan zabe da sauran gyare-gyaren hukumomi.
Dawowar wannan tsari ya zo ne yayin da shirye-shirye ke kara karfi kafin babban zaben 2027, inda ake sa ran ‘yan majalisa za su yi la’akari da gyare-gyaren zabe da sauran matakan da suka shafi tsarin zabe.
Ana sa ran shugabannin Majalisar Dattawa da ta Wakilai za su bayyana muhimman abubuwan da suka fi daukar hankali a majalisar yayin da ake fara zaman majalisar.
Ana kuma sa ran ‘yan majalisa za su fuskanci tambayoyi kan aiwatar da kasafin kudin 2026, ayyukan mazabu da sauran batutuwan da suka shafi al’umma.
A baya Majalisar Dokoki ta Kasa ta tsawaita hutunta domin ba da damar kammala aikin gyaran fuska a zauren majalisar dokoki.
Aisha.Yahaya, Lagos



