Zaben Gwamnan Jihar Osun: APC Ta Sanar Da Kwamitin Yakin Neman Zabe Na Kasa

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta sanar da kafa Kwamitin Yakin Neman Zabe na Kasa da kuma kananan kwamitoci domin zaben gwamnan jihar Osun da aka tsara gudanarwa a ranar 15 ga watan Agusta, 2026.
A cewar sanarwar da Sakataren Jam’iyyar na Kasa, Sanata Surajudeen Ajibola Basiru, ya sanya wa hannu, Gwamnan jihar Imo kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Jam’iyyar (Progressive Governors’ Forum), Hope Uzodimma, ne zai jagoranci Kwamitin Yakin Neman Zabe na Kasa.
Mataimakan shugaban kwamitin sun hada da Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni, Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas. Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Siyasa da Sauran Batutuwa, Ibrahim Kabir Masari, zai yi aiki a matsayin Mataimakin Shugaba, yayin da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin zai kasance Sakatare.
APC ta bayyana cewa kwamitin ya kunshi shugabannin jam’iyya, gwamnoni, mambobin Kwamitin Gudanarwa na Kasa, manyan jami’an Majalisar Dokoki ta Kasa, ministoci, ‘yan majalisa, da sauran masu ruwa da tsaki da aka dora wa alhakin jagorantar yakin neman zaben jam’iyyar a jihar Osun.
KARANTA KUMA: APC na Matakin Kawo Karshen Rikicin Anambra Gabanin Zaben 2027
Haka kuma, jam’iyyar ta kafa kananan kwamitoci na musamman domin kula da tsare-tsaren zabe, harkokin kudi, tattara goyon bayan jama’a a matakin tushe, harkokin dabaru da kayan aiki, yada labarai da wayar da kan jama’a, tsaro, tattara matasa da mata, harkokin masu nakasa, tsarin girmamawa da karbar baki (protocol), sa ido, da ayyukan sakatariya.
Za a kaddamar da Kwamitin Yakin Neman Zabe na Kasa da kananan kwamitocinsa a ranar Talata, 28 ga watan Yuli, 2026, a Cibiyar Taro ta Transcorp Hilton da ke Abuja, da misalin karfe 12 narana.
Aisha.Yahaya, Lagos



