Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Nada Olanrewaju Smart A Matsayin Mai Ba Da Shawara Na Musamman.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada Dr. Wasiu Olanrewaju-Smart a matsayin Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Majalisar Dokoki ta Kasa, musamman bangaren Majalisar Wakilai.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Kasa, Bayo Onanuga, ya fitar, an bayyana cewa Dr. Olanrewaju-Smart zai maye gurbin Ibrahim Olanrewaju, wanda ya yi murabus daga mukaminsa domin neman takarar wani mukami a jiharsa ta asali.

Olanrewaju-Smart kwararren masani ne a fannin tsare-tsaren gwamnati (public policy). Yana da digirin digirgir (PhD) a fannin Gudanarwar Ilimi daga Jami’ar Lead City da kuma digiri na biyu (Master’s) a fannin Gudanarwar Jama’a daga Jami’ar Harvard.

A halin yanzu, yana aiki a matsayin ‘Edward Mason Fellow’ a fannin tsare-tsaren gwamnati a Harvard Kennedy School. Wannan kwararre kan tsare-tsare, mai shekaru 40, ya taba rike mukamin ‘LEAPS Fellow’ a Cibiyar Fasaha ta Massachusetts (MIT), sannan yana da takardar shedar kwarewa ta musamman a fannin Hulda da Jama’a (Public Relations) daga London School of Public Relations.

KARANTA KUMA: Shugaba Tinubu zai halarci Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya na shekarar 2026

Bugu da kari, ya yi aiki a matsayin ‘Policy Fellow’ a kamfanin Quantum Alliance AI da ke Amurka, inda ya mayar da hankali kan hadewar fasahar basirar dan-adam (AI) da fasahar da ke amfanar al’umma (civic technology).

Ayyukansa a Majalisar Dokoki ta Kasa sun hada da mukamai daban-daban, tun daga Mataimaki kan Bincike da Yada Labarai ga Shugabannin ‘Yan Tsiraru da ‘Yan Rinjaye na Majalisar Wakilai a zaman majalisa na 7 da na 8, har zuwa mukaman Mataimaki na Musamman, Mataimakin Shugaban Ma’aikata, da kuma Shugaban Ma’aikata ga Kakakin Majalisar Wakilai a zaman majalisa na 9 da na 10.

Daga baya, Olanrewaju-Smart ya shiga fadar shugaban kasa a watan Oktoban 2023, a matsayin Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Kasa kan Harkokin Hadin Gwiwar Gwamnatoci (Intergovernmental Affairs), mukamin da ya rike har zuwa lokacin da aka yi wannan sabon nadin.

Ayyukansa na bincike kan tsare-tsaren gwamnati sun hada da gudummawa wajen samar da muhimman dokoki, kamar Dokar Lamunin Karatu mara Ruwa (Interest-Free Student Loan Act), da sauransu.

Shugaba Tinubu ya nuna kwarin gwiwar cewa Olanrewaju-Smart zai yi amfani da gogewarsa, hazakarsa, da kuma kwazonsa wajen inganta hadin gwiwar majalisa da kuma karfafa alaka mai amfani tsakanin Fadar Shugaban Kasa, Ma’aikatu, Sassan Gwamnati, da Hukumomi (MDAs) da kuma Majalisar Wakilai.

Wannan nadi ya fara aiki nan take.

 

 

Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button