Côte d’Ivoire Za Ta Karbi Bakuncin Taron Kasuwanci Na Amurka Da Afirka 2027

Kaba Niale Babban Minista kuma Ministan Harkokin Waje ta sanar cewa kasar Côte d’Ivoire ce za ta karbi bakuncin taron kasuwanci na Amurka da Afirka (U.S.-Africa Business Summit) a shekarar 2027.
Ta yi wannan sanarwar ne a gefen taron tattaunawa kan kasuwanci da zuba jari da kungiyar Corporate Council on Africa (CCA) ta shirya a Amurka.
Ta bayyana zabin birnin Abidjan a matsayin “alama ta nuna amincewa da kuma nauyi” ga kasar.
Ana sa ran wannan babban taro zai mayar da Côte d’Ivoire cibiyar kasuwanci da ke hada Amurka da nahiyar Afirka tare da zama ginshikin bunkasa zuba jari kasuwanci da hadin gwiwa mai muhimmanci tsakanin Washington da Afirka.
KARANTA KUMA: Côte d’Ivoire za ta karbi bakuncin taron yankin Afirka na farko kan harkokin ruwa
A cewar gwamnati wannan zabi yana nuna kyakkyawar alakar abota da hadin gwiwa a fannoni daban-daban tsakanin Côte d’Ivoire da Amurka.
A jawabinta Niale ta ambaci muhimman mutane ciki har da Franck Garcia Mataimakin Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka mai kula da harkokin Afirka da kuma Florizelle Liser Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa na kungiyar Corporate Council on Africa.
Ta ce “Zuba jarin Amurka a Côte d’Ivoire ya fara haifar da sakamako mai kyau” inda ta ambaci kamfanin Cybastion a fannin sauye-sauyen fasahar zamani (digitaltransformation) Starlink a fannin samar da intanet da kuma Zipline a fannin jigilar kayan kiwon lafiya.”
Ministar ta bayyana cewa Côte d’Ivoire na da burin mayar da alkawuran zuba jari zuwa zahirin ayyuka tare da karfafa gwiwar shugabannin kasuwanci a taron su shiga tattaunawa kai tsaye da kuma kulla kawance mai dorewa wanda zai biya bukatun al’umma.
Kasancewar za ta karbi bakuncin taron na 2027 ya tabbatar da matsayin Abidjan a matsayin muhimmiyar cibiyar tattalin arziki a Yammacin Afirka wanda ke nuna ci gaban hadin gwiwa mai karfi tsakanin Côte d’Ivoire da Amurka.



