Ebola A DRC: Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO) Ta Yi Gargadi Game Da Karancin Ma’aikatan Lafiya.

Jamhuriyar Demokradiyyar Congo na fuskantar karancin ma’aikatan kiwon lafiya da za su yi aiki a cibiyoyin kula da masu cutar Ebola yayin da kasar ke fama da barkewar cutar cikin sauri inda aka samu karuwar masu dauke da cutar da kashi 73 cikin dari a cikin makonni uku a lardin North Kivu.
Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargadi game da lamarin inda ta bayyana cewa har yanzu ba a iya shawo kan cutar ba duk da raguwar adadin masu dauke da ita a wasu lardunan.
Bisa alkaluman gwamnati na baya-bayan nan, cutar ta bazu zuwa larduna bakwai inda aka samu mutane 7,773 da aka tabbatar suna dauke da cutar tare da mutuwar mutane 3,759.
Daraktar WHO mai kula da ayyukan gaggawa a yankin Afirka Marie Roseline Belizaire ta ce an samu raguwar masu dauke da cutar da kashi 26 cikin dari a lardin Ituri da kuma kashi 15 cikin dari a lardin Haut-Uele tsakanin ranar 31 ga watan Agusta da 20 ga watan Satumba.
Sai dai Belizaire ta ce yanayin yadda cutar ke yaduwa ya ci gaba da bambanta sosai a yankunan da abin ya shafa.
“Yayin da ake samun raguwar masu dauke da cutar da mace-mace a wasu lardunan a wasu kuma ana ci gaba da samun karuwa. Har yanzu ba a shawo kan cutar ba kuma tana ci gaba da yaduwa a fadin yankuna masu fadi” in ji ta.
WHO ta ce rashin tsaro gudun hijirar jama’a yajin aikin ma’aikatan kiwon lafiya da kuma karuwar zirga-zirgar jama’a na kara dagula lamarin cutar.
Hukumar ta ce cutar na kan hanyar zarce annobar Ebola ta shekarun 2014-2016 a Yammacin Afirka wadda ita ce mafi muni a tarihi inda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da 11,000 musamman a kasashen Guinea Liberia da Sierra Leone.
Catherine Smallwood jami’ar WHO mai kula da harkokin cutar Ebola ta ce an fara samun raguwar masu dauke da cutar da mace-mace a lardin North Kivu bayan makonni da dama ana samun karuwa.
Ta ce duk da cewa ana kara yawan gadajen kula da marasa lafiya a kowace rana cibiyoyin kiwon lafiya na ci gaba da fuskantar karancin ma’aikata da abokan aiki da ake bukata wajen gudanar da ayyukansu.



