Wasanni

Super Eagles Sun Fara Shirye-Shiryen Neman Gurbin Shiga Gasar AFCON.

Kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles ta Najeriya ta kara kaimi wajen shirye-shiryen neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) na shekarar 2027 inda ‘yan wasa 23 suka halarci zaman horo na farko gabanin karawar da za su yi da Madagascar a ranar Juma’a.

An gudanar da zaman horon ne a filin wasa na Godswill Akpabio da ke Uyo inda babban koci Eric Chelle da mataimakansa suka fara shirya kungiyar yadda ya kamata domin wasan farko na rukunin L.

Mai tsaron ragar kungiyar Udinese Maduka Okoye shi ne kadai dan wasan da ake sa ran zai iso sansanin yayin da kyaftin Wilfred Ndidi da Samuel Chukwueze da Stanley Nwabali suka riga suka shiga tawagar jim kadan kafin fara zaman horon na yamma.

Daga cikin wadanda suka fara isa akwai Moses Simon Akor Adams Taiwo Awoniyi da kuma wadanda aka gayyata a karon farko, wato Isaac James Moses Usor da George Ilenikhena.

Emmanuel Fernandez Benjamin Fredrick Arthur Okonkwo Chibuike Nwaiwu Alex Iwobi Semi Ajayi Calvin Bassey da kuma dan wasan baya Ola Aina wanda ya dawo cikin tawagar suma suna cikin ‘yan wasan da ke sansanin.

Sauran ‘yan tawagar sun hada da Ademola Lookman Bright Osayi-Samuel Tolu Arokodare Bruno Onyemaechi Raphael Onyedika da Frank Onyeka.

Chelle ya gayyaci ‘yan wasa 24 domin fafatawa a wasan share fagen shiga gasar cin kofin duniya da Najeriya za ta fafata da Madagascar da Guinea-Bissau inda Eagles za ta karbi bakuncin Madagascar a Uyo ranar Juma’a, kafin ta tafi Bissau don wasanta na biyu a rukunin L a ranar 29 ga Satumba.

Za a bude sansanin ‘yan wasan Najeriya a hukumance ranar Litinin, kodayake yawancin ‘yan wasan sun isa kwana daya bayan fara horon farko.

Eagles za ta fara kakar wasa ba tare da dan wasan gaba na Galatasaray Victor Osimhen ba wanda ya janye daga tawagar domin ci gaba da murmurewa daga raunin da ya samu.

KARANTA KARIN BAYANI: Tauraron Super Eagles Osimhen Zai Rasa Wasannin Neman Gurbin Shiga Gasar AFCON.

Rashin kasancewarsa ya bude kofa ga Awoniyi Arokodare Adams da Ilenikhena su fafata domin samun damar taka leda a bangaren kai hari.

Najeriya tana cikin Rukuni na L tare da kasashen Madagascar Guinea-Bissau da Tanzania. Kasancewar an riga an tabbatar wa Tanzania gurbi a gasar ta shekarar 2027 a matsayin daya daga cikin kasashen da za su karbi bakuncin gasar tare sauran kasashen za su fafata ne domin samun tikitin cancanta daga rukunin.

Kungiyar Super Eagles za ta yi kokarin ganin ta sake samun gurbi a gasar ta nahiyar Afirka bayan ta kammala gasar AFCON ta 2025 a kasar Moroko da samun lambar tagulla.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button