Najeriya

Uwargidan Gwamnan Anambra Ta Taya Dalibai Murna Bisa Nasarar Da Suka Samu A Gasar Muhawara Ta Duniya

Uwargidan Gwamnan Jihar Anambra Dr. Nonye Soludo ta taya daliban makarantar sakandare guda biyar daga jihar murna bayan sun lashe gasar muhawara ta tsakanin Najeriya da Malaysia ta shekarar 2026 inda suka doke takwarorinsu na Malaysia da ci 2-1 a wasan karshe.

Wannan nasara ta jawo wa daliban da kuma kasar Najeriya karbuwa a matakin kasa da kasa tare da nuna irin kwarewar da matasan Najeriya ke da ita wajen yin fice a gasa na ilimi.

Dalibai biyar din wadanda aka zaba ta hanyar shirin ‘President’s Schools Debate Nigeria’ (PSDN) su ne: Nwigwe Okwuchukwu daga Community Secondary School Obosi Okechukwu Angel daga Mater Amabilis Secondary School Umuoji Ozoude Jude daga St. Michael’s Model Comprehensive Grammar School Nimo Ezeogidi Cyril daga Bubendorff Memorial Grammar School Adazi-Nnukwu da kuma Ibekaku Chikamso daga Capital City Secondary School Awka.

KARANTA KUMA: Matar Gwamnan Anambra Ta Yi Kira Da A Dauki Matakan Kare ‘Yar Yarinya

Gasar wacce ta fara a ranar 10 ga watan Nuwamba 2026 ta hada matasa masu muhawara don nuna kwarewarsu ta fannin tunani nazari mai zurfi fasahar gamsar da wasu da kuma iya gabatar da jawabi a gaban jama’a inda aka kammala ta da wani wasan karshe mai cike da zafi da gasa mai karfi.

Tawagar Najeriya ta kasance karkashin jagorancin Shugabar Hukumar Ilimin Basic ta Jihar Anambra (ASUBEB) Dr. Justina Anyadiegwu tare da Mai Gudanar da Gasar Muhawara ta Jihar Mrs. Amaka Anekwe da sauran jami’an gwamnati.

A cikin wata sanarwa ta taya murna Dr. Soludo ya bayyana kokarin da daliban suka yi a matsayin babban nasara da kuma abin alfahari ga Jihar Anambra da ma Najeriya baki daya.

Uwargidan Gwamna wacce kuma ita ce ta kafa shirin ‘Healthy Living with Nonye Soludo’ ta bayyana cewa zurfin tunani kwarin gwiwa da kuma bajintar da daliban suka nuna a fagen duniya sun tabbatar da irin karfin da matasan Najeriya ke da shi.

Ta ce “Dalibanmu matasa guda biyar masu hazaka sun kafa tarihi ta hanyar lashe gasar muhawara ta kasa da kasa tsakanin Najeriya da Malaysia a shekarar 2026. Bajintarsu ta musamman zurfin tunaninsu da kuma kwarin gwiwarsu a matakin duniya shaida ce ta irin gagarumin karfin da matasanmu masu ban sha’awa ke da shi.”

Ta danganta wannan nasara da irin saka hannun jari da gwamnatin Soludo ta yi a fannin ilimi musamman kokarin inganta muhallin karatu fadada damammaki da kuma bunkasa hazaka domin bai wa matasa damar fafatawa a matakin duniya.

A cewarta wannan nasara ta kara jaddada muhimmancin samar wa matasa dandamali da tallafin da ya dace domin su bunkasa kwarewarsu tare da cimma cikakken karfin da Allah ya ba su.

Ta kara da cewa “Ga ku matasa zakarunmu kun sanya jihar Anambra ta yi alfahari. Ku ci gaba da yin buri ku ci gaba da koyo kuma ku ci gaba da karya iyakokin da aka saba da su. Makomarku tana da haske kuma muna goyon bayanku dari bisa dari.”

Gwamnatin Jihar Anambra ce ta dauki nauyin shigar da tawagar a gasar ta kasa da kasa wanda hakan ya bai wa daliban damar wakiltar Najeriya da kuma nuna hazakarsu a wajen iyakokin kasar.

Nasarar ta nuna muhimmancin ci gaba da saka hannun jari a fannin ilimi shirye-shiryen muhawara a makarantu da kuma ci gaban matasa wajen karfafa tunani mai zurfi sadarwa da kuma kwarewar jagoranci tsakanin matasa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button