Uwar Gidan Shugaban Ƙasa Ta Yi Kira Ga Haɗa Gwiwa Domin Dorewar Zaman Lafiya

Uwargidan Shugaban Najeriya Oluremi Tinubu ta yi kira da a hada karfi da karfe domin wanzar da zaman lafiya a fadin kasar yayin da Najeriya ke shiga sauran kasashen duniya don bikin Ranar Zaman Lafiya ta Duniya ta 2026.
Uwargida Tinubu ta yi wannan kiran ne a cikin wani sako da ta fitar domin bikin ranar mai taken “Zuba Jari a Zaman Lafiya Ga Kowa Ko’ina Kowace Rana” tare da jaddada rawar da daidaikun mutane da al’ummomi ke takawa wajen ginawa da kuma ci gaba da zaman lafiya.
Ta ce “zaman lafiya mai dorewa yana bukatar sadaukarwa da kuma hadin kan kowa tana mai jaddada cewa zaman lafiya dole ne ya fara a gida ya kuma fadada zuwa makarantu wuraren aiki da kuma al’ummomi.”
KARANTA KUMA: Ranar Zaman Lafiya ta Duniya: NAF ta yi kira ga a samu jituwa da hadin kai.

A cewarta zaman lafiya yana ƙaruwa ta hanyar haƙuri haƙuri adalci girmama juna da tattaunawa.
Ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su rungumi waɗannan dabi’u tare da yin aiki tare don ci gaba da wanzuwar zaman lafiya a ƙasar.
Matar Shugaban Ƙasa ta kuma yi kira ga ‘yan ƙasa da su guji duk wani abu da zai raba ƙasar su zauna lafiya da juna.
“Ina ƙarfafa dukkan ‘yan Najeriya da su ƙi rabuwa su rungumi dabi’un da ke haɗa mu a matsayin mutane ɗaya. Bari mu zuba jari a cikin zaman lafiya ta hanyar kalamanmu zaɓinmu da ayyukanmu kowace rana. Barka da Ranar Zaman Lafiya ta Duniya ta 2026″ Ta ƙara da cewa.
Ana bikin Ranar Zaman Lafiya ta Duniya kowace shekara a ranar 21 ga Satumba. Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya ya kafa ranar a shekarar 1981 yayin da a shekarar 2001 ya sanya ranar a matsayin lokacin rashin tashin hankali da tsagaita wuta.
Mai Girma Sanata Oluremi Tinubu CON Uwargidan Shugaban Tarayyar Najeriya



