Yan sandan Gombe sun ƙarfafa tsaro gabanin zaɓen cike gurbi na mazabar tarayya.

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Gombe ta sanar da daukar cikakkun matakan tsaro gabanin zaben cike-gurbi na mazabar Tarayya ta Gombe Kwami Funakaye wanda aka tsara gudanarwa a ranar Asabar 19 ga watan Satumbar 2026.
Rundunar ta bayyana cewa ta tura isassun jami’ai da kayan aiki zuwa ofisoshin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) cibiyoyin tattara sakamakon zabe rumfunan zabe da sauran muhimman wurare a kananan hukumomi ukun da abin ya shafa.
A cikin wata sanarwa Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Gombe CP Umar Ahmed Chuso ya bayyana cewa ana gudanar da wannan aiki ne tare da hadin gwiwar mambobin Kwamitin Tuntuɓa na Hukumomi daban-daban kan Tsaron Zabe (ICCES) domin tabbatar da gudanar da zaben cikin lumana kafin yayin da kuma bayan kammala kada kuri’a.
KARANTA KUMA: INEC ta Kara Kaimi Wajen Shirye-Shiryen Karshe Na Zaɓen Cike Gurbi A Gombe.
Ya bayyana cewa za a takaita zirga-zirga da harkokin kasuwanci a kananan hukumomin Gombe Kwami da Funakaye daga karfe 6 na safe zuwa karfe 6 na yamma a ranar Asabar ban da ayyukan da suka zama dole a matsayin wani bangare na matakan tsaro.
Kwamishinan ‘yan sandan ya ce ba za a bai wa ma’aikatan da ke gudanar da ayyukan da suka zama dole damar amfani da kararrawar gaggawa (siren) motocin da ba su da rajista ko motocin da aka rufe lambobin rajistarsu ba.
Hukumar ta kuma fayyace cewa hukumomin tsaro na gwamnati da ke aiki karkashin tsarin ICCES ne kawai za su samu izinin samar da tsaro yayin zaben.
Ta kuma bayyana cewa an cire kungiyoyin tsaro na jiha kungiyoyin da ke taimakawa wajen tsaro masu gadin kamfanoni masu zaman kansu da kungiyoyin sa kai (vigilante) daga ayyukan tsaron zaben.
‘Yan sandan sun yi gargadi game da yada labaran karya ayyukan ‘yan daba na siyasa da sauran ayyukan da za su iya kawo cikas ga zaman lafiyar jama’a yayin zaben.
Sun kuma yi gargadin cewa ba za a amince da nuna makamai ko mallakar abubuwan da za su iya haifar da tuhuma a wuraren kada kuri’a ba.
Rundunar ‘Yan sandan Jihar Gombe ta bukaci iyaye da masu kula da yara da su yi taka-tsantsan ga ‘yan uwansu da ke barin a dauke su aiki ko kuma a yi amfani da su a matsayin ‘yan daba na siyasa.
A cewar rundunar duk wanda aka samu yana aikata ayyukan da ka iya kawo cikas ga gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali za a kama shi kuma a gurfanar da shi a gaban kuliya.
‘Yan sandan sun kuma bukaci mazauna yankin da su hada kai da hukumomin tsaro tare da kai rahoton ayyukan da ake zargi ga ofishin ‘yan sanda mafi kusa ko ta hanyar lambobin gaggawa na rundunar: 0815 056 7771 da 0903 643 5359.



