Birtaniya Za Ta Ci Gaba Da Buɗe Ofishin Jakadancin Kudus

Ministan harkokin wajen Birtaniya Ed Miliband ya bayyana a ranar Alhamis cewa ofishin jakadancin kasar (Consulate General) da ke Gabashin Kudus wanda Isra’ila ta ba da umarnin rufe shi zai ci gaba da kasancewa a bude a matsayin ofishin wakilcin Birtaniya mai zaman kansa da ke gudanar da ayyuka domin yi wa al’ummar Falasdinu hidima.
Isra’ila ta ba da umarnin rufe ofishin jakadancin Birtaniya da ke Gabashin Kudus a ranar Alhamis bayan da London ta sanar da shirinta na kakaba takunkumai kan matsugunan Yahudawa da ke yankin Yammacin Kogin Jordan (West Bank).
Miliband ya ce bayan an janye wasu ma’aikata da iyalansu a ‘yan makonnin da suka gabata yanzu za su yi aiki don sake karfafa kasancewarsu a wurin.
KARANTA KUMA: http://Isra’ila ta ba da umarnin rufe ofishin jakadancin Birtaniya a Kudus
Tabarbarewar dangantaka tsakanin wadannan kawaye biyu ta haifar da hasashe a Isra’ila cewa Birtaniya na iya mayar da martani kan matakin rufe ofishin ta hanyar korar jami’an diflomasiyyar Isra’ila daga London.
“Za mu yi aiki a watanni masu zuwa don sake gina da karfafa kasancewarmu kuma ba za mu dauki matakin ramuwar gayya ba yayin da ake ci gaba da tattaunawa mai ma’ana kan lamarin” in ji Miliband.
Ministan Birtaniya mai kula da harkokin Gabas ta Tsakiya Stephen Doughty ya bayyana cewa Birtaniya na ci gaba da tattaunawa da gwamnatin Isra’ila kuma tana matukar nuna rashin jin dadinta game da matakin da Isra’ila ta dauka kan ofishin jakadancinta.
“Gininmu yana nan a bude, kuma ma’aikatanmu na ci gaba da gudanar da muhimman ayyuka” in ji Stephen Doughty yayin da yake zantawa da tashar Sky News. “Muna nan a Kudus… kuma yana da matukar muhimmanci a ci gaba da gudanar da wannan aiki.”



