Shugabannin APC ADC NDC Sun Ziyarci Zamfara Domin Ta’aziyyar Yari

Manyan ‘yan siyasa daga jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da sauran jam’iyyun adawa sun hallara a Talata Mafara Jihar Zamfara domin yin ta’aziyya ga tsohon Gwamnan Jihar Zamfara kuma Darakta-Janar na kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar APC Sanata Abdulaziz Abubakar Yari bisa rasuwar kanwar mahaifiyarsa Hajiya Rukiya Jibril.
Wannan ziyarar ta’aziyya ta hada manyan jami’an gwamnatin tarayya shugabannin jam’iyyar APC da fitattun ‘yan siyasar adawa lamarin da ya nuna yadda aka samu wakilcin bangarorin siyasa daban-daban a wurin zaman makokin iyalin.
Wanda ya jagoranci tawagar gwamnatin tarayya shi ne Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) Sanata George Akume wanda ya isar da sakon ta’aziyyar Shugaba Bola Tinubu ga Yari da iyalansa.
Akume ya tabbatar wa iyalin mamaciyar cewa ba su kadai ba ne a wannan lokaci na bakin ciki inda ya bayyana mutuwa a matsayin wani mataki na sauyi da komawa ga Allah bisa ga nufinsa da hikimarsa.
Ya bukaci iyalin su samu karfin gwiwa daga imaninsu da kuma sanin cewa mamaciyar ta kammala tafiyarta a duniya tare da komawa ga Mahaliccinta.
KARANTA KUMA:http://Zamfara na Neman Asusun Tallafawa Wadanda Rikici ya Shafa Domin Gina Zaman Lafiya
Sakataren Gwamnatin Tarayya ya yi addu’ar Allah ya gafarta wa Hajiya Rukiya tare da yi mata rahama ya karbi ayyukanta na kwarai ya kuma sanya ta cikin bayin Allah na kwarai.
Yayin karbar tawagar Yari ya nuna godiyarsa ga Shugaba Tinubu bisa nuna damuwa da goyon baya ga iyalin.
Ya kuma gode wa Akume da sauran mambobin tawagar bisa tafiyar da suka yi zuwa Talata Mafara domin girmama mamaciyar da kuma taya iyalin zaman makokin.
Samun Nutsuwa da Karfin Gwiwa
Yari ya bayyana cewa ziyarar ta ba shi da iyalinsa nutsuwa karfin gwiwa da kuma juriya yayin da yake yi wa Shugaban kasa SGF da mambobin tawagar addu’ar ci gaba da samun shiriyar Allah da albarkarsa.
Ya yi kira ga ‘yan Najeriya su rika tunawa da goggonsa a cikin addu’o’insu tare da neman Allah ya gafarta mata ya yi mata rahama ya kuma sanya ruhinta ya huta cikin kwanciyar hankali.
Daga cikin wadanda suka raka Akume akwai Gwamnan Jihar Neja Umar Bago Sakataren Jam’iyyar APC na kasa Sanata Ajibola Bashiru tsohon Gwamnan Jihar Imo Sanata Rochas Okorocha da tsohon Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Taron ya kuma samu halartar fitattun mutane daga jam’iyyun siyasa na adawa. Tsohon Gwamnan Jihar Sokoto Sanata Aminu Waziri Tambuwal tare da rakiyar Sanata Abdul Ningi sun wakilci jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) yayin da Sanata Tony Nwoye ya jagoranci tawagar jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC).
Hajiya Rukiya Jibril ita ce ƙanwar mahaifiyar Sanata Yari ta jini.



