Duniya

Tarayyar Turai Ta Saki Kadarorin Rasha Da Aka Dakatar Zuwa Ukraine

Hukumar Tarayyar Turai (EU) ta sanar a ranar Laraba da ta gabata, cewa za ta ware Yuro biliyan 1.4 (dalar Amurka biliyan 1.6)—kudaden da aka samu daga ribar dukiyar Rasha da aka dakatar da amfani da ita—domin tallafawa Ukraine.

Hukumar ta bayyana cewa an samo wadannan kudade ne daga ribar da aka samu kan kudaden da ke cikin asusun babban bankin Rasha, wadanda Tarayyar Turai ta dakatar da amfani da su bayan da Rasha ta mamaye Ukraine.

An mika kudaden ga kungiyar ne a ranar 3 ga watan Agusta. Shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, ta bayyana cewa ya kamata Rasha ta dauki alhakin barnar da yakin ya haifar.

KARANTA KUMA: ‘Yan Majalisar Tarayyar Turai na neman kafa Kungiyar Tsaro ta Turai

“Dole ne Rasha ta biya diyyar barnar da ta haifar. Kuma muna amfani da kudaden da aka samu daga dukiyar Rasha da aka dakatar da amfani da ita domin tabbatar da hakan,” in ji von der Leyen.

Ta bayyana cewa za a samar da karin wadannan kudade ga Ukraine domin karfafa karfinta na ci gaba da jurewa yakin da ake yi.

“Muna samar da karin Yuro biliyan 1.4 daga cikin kudaden ga Ukraine.

Wannan zai tallafawa Ukraine wajen ci gaba da tsayayya ga yakin da Rasha ke yi ba bisa ka’ida ba,” in ji von der Leyen.

Wannan sabon matakin na daga cikin kokarin da Tarayyar Turai ke yi na samar da tallafin kudi ga Ukraine, ta hanyar amfani da kudaden da aka samu daga dukiyar gwamnatin Rasha da aka dakatar da amfani da ita a cikin kasashen kungiyar.

 

 

Reuters/Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button