Sarakunan Gargajiya Da Shugabannin Addini Sun Goyi Bayan Shirin Kalu Na Sake Tsayawa Takara Shekarar 2027

An ci gaba da samun goyon baya ga Mataimakin Kakakin Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu, kafin babban zaben 2027, inda sarakunan gargajiya da shugabannin addini a karamar Hukumar Bende ta Jihar Abia suka bayyana goyon bayansu ga takararsa ta wa’adi na uku a Majalisar Dokoki ta Kasa.
Masu goyon bayan na baya-bayan nan sun fito ne daga Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Umunna, wanda hakan ya kara nuna goyon bayansu ga Kalu a fadin mazabar.
Wannan ci gaba ya biyo bayan amincewar Mataimakin Shugaban Majalisar da Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Jihar Bende ta Kudu (Ikwuisi) ta yi kwanan nan, wadda ta kuma yi watsi da ikirarin shirin raba-gari da wasu masu ruwa da tsaki suka gabatar.
An kuma samu goyon baya ga Kalu daga wasu kungiyoyi a cikin mazabar, ciki har da Dandalin Siyasa na Bende, mata ‘yan kasuwa da masu babura na kasuwanci, wadanda suka ambaci tsoma bakinsa na majalisa da ayyukan mazabu a matsayin dalilan da suka sa ya sake tsayawa takara.
KARANTA KUMA: Mataimakin Shugaban Majalisa Kalu ya tura shirin tsaro da Afirka ke jagoranta.

An bayyana wannan goyon baya ne yayin rangadin tuntubar al’umma da Kalu ke gudanarwa mai taken “Haɗuwa da Mutanen Mazabarku” (Meet Your Constituents); shiri ne da yake amfani da shi wajen tattaunawa da al’ummomi da masu ruwa da tsaki domin bayar da rahoton ayyukansa, jin ra’ayoyinsu, da kuma tattauna muhimman ayyukan ci gaba da ake bukata.
A wani taro da aka gudanar a fadar Eze Kalu Okorie Ezeukwu da ke Bende, shugabannin gargajiya sun yaba wa Mataimakin Kakakin Majalisar bisa irin kwazon da ya nuna, tare da bayyana goyon bayansu baki daya ga kudirinsa na neman wa’adi na uku.
Da yake jawabi a madadin sarakunan, Eze Kalu Okorie ya bayyana cewa Kalu ya kawo muhimman ayyuka da tallafi ga yankin Bende, inda ya kara da cewa masarautun gargajiya suna alfahari da nasarorin da ya samu.
Haka kuma, Eze Innocent Kalu Mba ya bayyana Kalu a matsayin dan majalisa mafi kwazo da ya taba wakiltar mazabar Bende a matakin tarayya, yana mai nuni da cewa yadda ake ganin rawar da yake takawa da kuma nasarorin da ya samu a Majalisar Dokoki ta Tarayya sun sanya jama’a alfahari.
“Mu da muke karanta labarai da kallon talabijin muna matukar alfahari da shi. Ba za mu iya barin wanda ya cimma irin nasarorin da ya samu ba, mu zabi wanda ba ya yin komai (mai zaman banza). Benjamin Kalu ya kawo wa al’ummar Umunna amfanin dimokuradiyya. Me kuma muke nema? Bari mu ba shi cikakken goyon baya da hadin kai. Zai zama babban rashi idan muka rasa Benjamin Kalu. Shi ne abin alfaharin Bende kuma ya kamata ya ci gaba da wakiltarmu. Ina kira ga dukkan mutanenmu; babu wanda ya fi Benjamin Kalu. Ya gina asibitoci, makarantu, da hanyoyi. ‘Yan uwana sarakuna, bari mu goyi bayan danmu. Shi kadai ne ya yi mana wani abu,” in ji shi.
Sarakunan sun kuma yi watsi da rade-radin cewa akwai tsarin karba-karba da ke nufin cire Kalu daga kujerar wakilcin mazabar Bende ta tarayya, inda suka jaddada cewa matsayinsu ya dogara ne kan kwazonsa da kuma ci gaban da aka samu a yankin.
Da yake mayar da martani, Kalu ya gode wa shugabannin gargajiya da na addini bisa goyon baya da amincewar da suka nuna masa, inda ya bayyana wannan goyon baya a matsayin tabbacin cewa matakin da ya dauka na neman sake tsayawa takara ya dace.

“Muna kan tafiyar samun ci gaba. Kun yi zabin da ya dace na tura ni Majalisar Wakilai don wakiltarku. Ina matukar godiya da farin ciki da na sanya ku alfahari. Ana ganin sakamakon aikin. Dubi ayyukan da na kawo yankinmu; akwai karin wasu da za su zo. Ina son Bende. Ina son mutanena. Shin kun san ma’anar kawo cibiyoyin gwamnatin tarayya guda biyu zuwa karamar hukuma daya? Wannan yana faruwa ne a lokacinku. Kowace cibiya daga cikinsu za ta samar da ayyukan yi ga mutane akalla 3,000. Hakan zai kawo ci gaba,” in ji Mataimakin Kakakin Majalisar yana mai jaddada hakan.
A matsayin wani bangare na mu’amalarsa da shugabannin gargajiya, Mataimakin Kakakin ya bayar da kyautar motocin bas ga Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Umunna da kuma Majalisar Sarakunan Gargajiya ta yankin Bende ta Kudu (Ikwuisi) domin tallafawa ayyukansu.
Ya kuma tabbatar wa al’umma cewa za a ci gaba da kawo karin ayyukan ci gaba zuwa yankin.
A wani taro daban da aka gudanar a Babban Cocin Methodist da ke Uzuakoli, shugabannin addini suma sun nuna goyon bayansu ga kudirin Kalu na neman wa’adi na uku.
Bishop James A. Anyanwu na Diocese ta Methodist ta Uzuakoli da Bishop Nwaulo Ikechukwu Emezie na Diocese ta Methodist ta Item ne suka jagoranci taron.
Shugabannin cocin sun bayyana damuwarsu game da rashin kulawar da ya kamata daga bangaren gwamnati ga wasu cibiyoyi da wuraren da coci ta kafa don hidimtawa al’ummar Bende, tare da yin kira ga Mataimakin Kakakin da ya shiga tsakani.
Da yake mayar da martani, Kalu ya tabbatar musu cewa za a sanya bukatunsu cikin tsare-tsaren ci gaban yankin.
Ya kara bayyana cewa an tanadi kudade a cikin kasafin kudi domin ayyukan ci gaban matasa a dukkan sassan yankin, inda ya yi nuni da cewa za a shirya wani taron kwararru tare da shugabannin addini kimanin 130 domin tattaunawa kan wasu ayyuka da aka zaba.

Daga bisani, shugabannin cocin sun nuna goyon bayansu ga kudirin Kalu na neman wa’adi na uku a Majalisar Wakilai.
Wannan goyon baya ya kara karfafa matsayin Mataimakin Kakakin a fadin Bende, yayin da hukumomin gargajiya, kungiyoyin addini, da kungiyoyin al’umma suka ambaci irin rawar da ya taka wajen wakilci da ayyukan ci gaba a matsayin dalilan da suka sa su goyi bayan dawowarsa Majalisar Dokoki ta Kasa.
Aisha.Yahaya, Lagos



