Fitattun LabaraiNajeriya

Najeriya Ta Fara Gyaran Cibiyoyin Horar da ‘Yan Sanda Guda 13

Gwamnatin Najeriya ta bayar da kwangilolin gyaran cibiyoyin horar da ‘yan sanda guda 13 a sassa daban-daban na kasar.

An tsara shirin gyaran wanda zai dauki tsawon makonni uku domin shirya wadannan cibiyoyi don fara shirye-shiryen horarwa na rundunar ‘yan sandan Najeriya.

An gabatar da wannan sabon bayani ne a ranar Alhamis a Abuja yayin taron Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa (NEC) karo na 160 wanda Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya jagoranta.

Da yake yi wa manema labarai bayani bayan kammala taron Gwamnan Jihar Ondo Lucky Aiyedatiwa ya bayyana cewa “wannan mataki ya yi daidai da kudirin gwamnatin Najeriya na ba da karin kulawa ga horar da jami’an Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya.”

Gwamna Aiyedatiwa ya jaddada cewa gwamnati ta sa ido sosai wajen inganta ayyukan rundunar ‘yan sandan kasar ta hanyar samar da ingantaccen horo ga ma’aikatanta.

Ya ce “Majalisar Tattalin Arziki ta Kasa ta samu bayani daga kwamitinta na musamman da ke kula da gyaran cibiyoyin horar da ‘yan sanda inda aka sanar da ita cewa an riga an fara aiwatar da matakan da suka dace domin cimma burin inganta yanayin wadannan cibiyoyi.”

“An kuma sanar da Majalisar cewa an riga an bayar da kwangilolin gyaran cibiyoyi 13 a sassa daban-daban na kasar kuma kashi 80 cikin 100 na ‘yan kwangilar sun riga sun karbi takardun amincewa da kwangilolin nasu.”

KARANTA KUMA: Mataimakin Shugaban Kasa Shettima ya bukaci Majalisar Tattalin Arziki ta ci gaba da aiwatar da gyare-gyare.

Mataimakin Gwamnan Jihar EnugU Ifeanyi Ossai wanda shi ma ya yi magana kan lamarin, ya bayyana cewa “nan ba da jimawa ba za a saki ƙarin kuɗaɗe ga ‘yan kwangilar.”

“Ma’aikatar Kuɗi ta yi alkawarin cewa nan da mako mai zuwa za a saki sauran kuɗaɗen da ake buƙata don biyan ‘yan kwangilar DA kuma Majalisar na sa ran cewa ‘yan kwangilar da aka zaɓa za su gudanar da ayyukan da aka damka musu cikin hanzari kamar yadda kwangilar ta tanada” in ji shi.

Har ila yau Mista Ossai ya ba ‘yan Najeriya tabbacin cewa za a ci gaba da gudanar da horo ga jami’an ‘yan sanda inda ya ƙara da cewa dukkan ‘yan ƙasa suna da rawar da za su taka wajen tabbatar da tsaron ƙasa ta hanyar ba da bayanai da haɗin kai ga jami’an hukumomin tsaro.

 

 

LADAN NASIDI.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button