
Rahotanni sun ce hukumomin tsaron Libya sun gano gawarwakin akalla bakin haure shida a kudu maso gabashin kasar bayan da motarsu ta lalace a hamada.
An gano gawarwakin a wani yanki na hamada kimanin kilomita 200 mil 124 arewa maso yammacin Jalu a cewar Hukumar.
An gano gawawwaki biyu a cikin motar da ta lalace yayin da aka gano wasu uku kimanin kilomita hudu mil 2.5. An gano wani gawa kimanin kilomita 10 mil shida daga motar bayan da jami’an tsaro suka bi diddigin sawun motar cewar Hukumar.
Ta ce takardun motar sun nuna cewa mai ita ya fito ne daga Chadi.
KARANTA KUMA: Sama da bakin haure 100 sun isa Girka daga Libya
Hukumar ta kuma ce an ceto bakin haure 19 a ranar Lahadi dangane da lamarin kodayake ba ta fayyace inda aka same su ba.
A cewar dan uwan mai motar wanda yana cikin bakin haure 19 da aka ceto wata motar da ke tafiya tare da kungiyar ta dauki mai daga motar da ta makale ta ci gaba da tafiyarta.
Libya ta zama babbar hanyar sufuri ga ‘yan cirani da ke tserewa daga rikici da talauci waɗanda ke neman isa Turai ta hanyar ketare hamada mai haɗari da Tekun Bahar Rum.
Kasar ta ga karuwar zirga-zirgar ‘yan cirani tun bayan boren da NATO ta yi a shekarar 2011 wanda ya hambarar da shugaban da ya daɗe yana mulki Muammar Gaddafi.
Hotunan da Hukumar ta fitar sun nuna jami’an tsaro tare da rakiyar membobin Bataliyar Biyar ta Rundunar Soja ta 129 suna dawo da gawawwakin tare da sanya su a cikin baƙaƙen jaka na filastik.
Reuters/Sulaiman Ibrahim Muhammad.



