Fitattun LabaraiNajeriya

Shugaba Tinubu Ya Amince Da Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa Na APC

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) domin zaben watan Janairun 2027.

Shugaban kasa ne zai jagoranci kwamitin a matsayin Shugaba yayin da Mataimakin Shugaban kasa Kashim Shettima da Shugaban jam’iyyar APC na kasa Farfesa Nentawe Yilwatda za su yi aiki a matsayin mataimakan shugaban kwamitin.

An bayyana cikakkun bayanai game da kwamitin yakin neman zaben a cikin jerin sunayen da aka fitar da safiyar Asabar wadanda kuma ke dauke da sa hannun Mashawarcin Shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru Mista Bayo Onanuga.

An nada tsohon Gwamnan jihar Zamfara Sanata Abdulaziz Yari a matsayin Darakta-Janar na yakin neman zaben yayin da Gwamnan jihar Imo Hope Uzodimma zai yi aiki a matsayin Sakatare. An kuma nada Sakataren jam’iyyar APC na kasa Sanata Ajibola Bashiru da Hadiza Bala-Usman a matsayin mataimakan sakatare.

Kwamitin yana kuma da tawagar masu ba da shawara da suka hada da Cif Bisi Akande da Cif Segun Osoba da Sanata Rochas Okorocha da Sanata Abdullahi Adamu da Sanata Florence Ita-Giwa.

 

KARANTA KUMA: APC ta kaddamar da kwamitin yakin neman zaben gwamna a jihar Anambra

 

An kuma dora wa Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abass da Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni tare da Sanatoci Opeyemi Bamidele da Jibril Barau nauyin zama mataimakan Darakta-Janar na yakin neman zaben a yankunan Kudanci da Arewacin kasar.

Sanata Adams Oshiomhole zai yi aiki a matsayin mataimakin Darakta-Janar mai kula da harkokin tara jama’a da hada kan magoya baya (mobilisation) yayin da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban kasa Femi Gbajabiamila zai kula da harkokin gudanarwa a matsayin mataimakin Darakta-Janar.

James Abiodun Faleke ya dawo cikin tsarin yakin neman zabe a matsayin Mataimakin Darakta-Janar mai kula da Tsare-tsare Daidaitawa da Sanya-ido kan Zabe.

Zai yi aiki tare da daraktocin shiyyoyi wadanda suka hada da Sanata Olushola Adeyeye (na Kudu-maso-Yamma) Dr. Ngozi Olejeme (na Kudu-maso-Kudu) Sanata Uche Ekwunife (na Kudu-maso-Gabas) Muntaqha Rabe (na Arewa-maso-Yamma) Ahmed Muhammed Ketso (na Arewa ta Tsakiya) da kuma Sanata Sani Danladi (na Arewa-maso-Gabas).

Muiz Adeyemi Banire ne zai jagoranci Sashen Shari’a tare da Dr. Liman Hassan da Babatunde Ogala a matsayin mataimakansa. Sauran mambobin sun hada da Prince Lateef Fagbemi tsohon Gwamna Ibrahim Shema Worgu Boms da Dr. Kingsley Tochukwu Udeh.

An nada Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a Mohammed Idris Malagi a matsayin Darakta mai kula da harkokin yada labarai da sadarwa ta dabarun siyasa, tare da Dr. Dele Alake da Bayo Onanuga da Lanre Issa-Onilu.

 

Sashen Yada Labarai ya kuma kunshi Tunde Rahman da Sunday Dare Daniel Bwala da Felix Morka a matsayin Mataimakan Daraktoci masu kula da daidaita ayyuka yayin da Abdulaziz AbdulAziz da Temitope Ajayi da Arabinrin Aderonke da Frederick Nwabufor za su yi aiki a matsayin Sakatarori masu kula da daidaita ayyuka.

Segun Dada ya dawo a matsayin Daraktan Sabbin Kafafen Yaɗa Labarai mukamin da ya riƙe a lokacin kamfen ɗin 2022 inda Solomon Arowolo ya zama Sakatare. Yaƙin neman zaɓen ya kuma naɗa masu magana da yawun jam’iyyar guda biyar ƙarƙashin jagorancin Dele Alake tare da Alwan Hassan Ayobami Oyalowo Kemi Asekun-Shittu da Adamu Fanda.

Shugaba Tinubu ya umarci ‘yan majalisar da su yi aiki don tabbatar da nasarar APC a zaɓen Janairun 2027 sannan ya yi kira ga shugabannin daraktoci da su haɗa sauran ‘yan jam’iyyar da ba a sanya sunayensu a hukumance ba.

 

Shugaban ya ce gwamnatinsa ta cika manyan alkawuran yaƙin neman zaɓe kuma ta sanya Najeriya a kan hanyar ci gaban tattalin arziki yana mai bayyana kwarin gwiwar cewa fa’idodin gyare-gyaren da ake ci gaba da yi sun fara bayyana.

 

 

Ladan Nasidi.

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button