Najeriya Za Ta kwaso karin ‘Yan kasarta Daga Afirka Ta Kudu

Ana sa ran wani sabon rukuni na ‘yan Najeriya su 83 su isa Legas daga Afirka ta Kudu a ranar Laraba, 19 ga watan Agusta, 2026, biyo bayan sabbin kokarin taimaka wa ‘yan Najeriyar da ke fuskantar barazanar kyamar baki da ke karuwa a kasar.
Mai magana da yawun Ma’aikatar Harkokin Waje Kimiebi Ebienfa wanda ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ya ce wadanda ake dawo da su za su isa Filin Jirgin Sama na Duniya na Murtala Mohammed da ke Legas ta hanyar jirgin saman kamfanin South African Airways.
Ebienfa ya ce ana sa ran jirgin zai tashi daga Filin Jirgin Sama na Oliver Tambo da ke Johannesburg da misalin karfe 3:35 na yamma agogon wurin sannan ya isa Legas da misalin karfe 8:45 na dare.
Ya bayyana cewa an samu damar gudanar da wannan aikin kwaso mutanen ne sakamakon shiga tsakani da kuma daukar nauyin tikitin jirgin da wasu mutane masu zaman kansu masu kishin al’umma suka yi.
KARANTA KUMA: Najeriya Ta Kwato Karin ‘Yan Kasa 271 Daga Afirka Ta Kudu
A cewarshi wannan ci gaban ya zo ne bayan kammala shirin gwamnatin tarayya na mayar da ‘yan Najeriya kusan 1,490 daga Afirka Ta Kudu a lokacin hare-haren kin jinin Afirka da kuma nuna kyamar baki.
Kakakin ma’aikatar ya ce gwamnati ta ci gaba da jajircewa wajen kare ‘yan Najeriya yana mai jaddada cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na daukar ‘yan Najeriya a kasashen waje a matsayin muhimman masu bayar da gudummawa ga ci gaban kasa.
“‘Yan Najeriya a kasashen waje ba su da nauyi amma muhimman kadarori ne ga ci gaban kasa” in ji shi yayin da yake sake jaddada jajircewarsu ga kare su da walwalarsu.
Ebienfa ya kuma yaba wa daidaikun mutane da masu hannu da shuni wadanda suka dauki nauyin sabon mayar da ‘yan Najeriya gida yana mai kira ga kungiyoyin kamfanoni masu zaman kansu da dagwamnatocin jihohi da ‘yan Najeriya masu kyawawan halaye a gida da waje da su yi koyi da wannan karamci tare da karfafa karfin kasar na mayar da martani ga gaggawar ofishin jakadanci.
Game da dangantakar Najeriya da Afirka ta Kudu Ebienfa ya bayyana cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da tattaunawa da hukumomin Afirka ta Kudu domin magance tushen matsalar kyamar ‘yan Afirka (Afrophobia) da kuma dakile hare-haren da ake kai wa ‘yan Najeriya.
Ya ce gwamnatin ta kuduri aniyar tabbatar da cewa an “dakile tare da yin Allah-wadai mai tsauri” game da duk wani nau’i na tashin hankali ko nuna wariya idan sun faru tare da daukar matakan hukunta wadanda suka aikata hakan.
LADAN NASIDI



