Shugaba Tinubu Ya Dawo Da Danjuma Babban Sakataren Ma’aikatar Kudi Da Aka Dakatar Kan Mukaminsa

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da dawo da M.S. Danjuma Sakataren Dindindin a Ma’aikatar Kudi mai kula da Ayyuka na Musamman kan aikinsa bayan an dage dakatarwar da aka yi masa sakamakon wani bincike da ke gudana.
Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya Olumuyiwa Enitan Abel ne ya sanar da amincewar Shugaban a cikin wata wasika mai dauke da kwanan wata 22 ga watan Oktoba 2026.
An dakatar da Danjuma ne a ranar 21 ga watan Agusta 2026 tare da wasu Sakatarorin Dindindin guda biyu biyo bayan wani rahoto daga Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka masu Alaka da hakan (ICPC).
KARANTA KUMA: Shugaba Tinubu Ya Mayar Da Dembos Kan Mukaminsa Na Darakta Janar Na NTA Tare Da Kirawo Tawagarsa
Rahoton ya shafi ayyukan wata kungiya ko hukuma da ake zargin kirkirar ta mai suna ‘Ofishin Aikin Musamman na Ci Gaban Al’amuran Kasuwanci na Ƙasa da Kayayyakin da aka Kera a Najeriya’ wacce ake zargin George Buchi Nwabueze ne ya ingiza ta tare da zargin cewa wasu ma’aikatan gwamnati a Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya na da hannu a ciki.
Bayan gudanar da cikakken bincike Shugaba Tinubu ya dage dakatarwar da aka yi wa Danjuma tare da umartar sa da ya koma kan ayyukansa na hukuma bisa la’akari da Dokokin Aikin Gwamnati ka’idojin da suka dace da kuma ka’idojin da’a da ke tafiyar da Aikin Gwamnatin Tarayya.
Wannan komawa kan aiki ta fara aiki ne tun daga ranar 21 ga watan Oktoba 2026.



