ECOWAS Da AU Sun Daidaita Tsarin Samar Da Zaman Lafiya Mai Mayar Da Hankali Kan Matasa

Kungiyar Tarayyar Afirka (AU), tare da Kungiyoyin Tattalin Arziki na Yankuna (RECs) da Hukumomin Yankuna (RMs), sun gudanar da taro a Gaborone, Botswana, domin nazarin halin da ake ciki da kuma rawar da matasa ke takawa wajen tsara matakan tunkarar kalubalen zaman lafiya da tsaro da ke tasowa a fadin nahiyar.
A cikin wata sanarwa da aka wallafa a shafin yanar gizo na Hukumar ECOWAS, an bayyana cewa taron na kwana biyu ya bai wa mahalarta cikakken bayani game da ci gaban da Hukumar Tarayyar Afirka ta samu wajen aiwatar da Tsarin Nahiyar Afirka kan Matasa, Zaman Lafiya da Tsaro (CFYPS) da kuma Shirin Aiwatarwa na shekaru 10, tun bayan taron daidaitawa na karshe tsakanin AU da RECs/RMs a shekarar 2023.
Taron ya kuma bayyana muhimman ayyuka da tsare-tsare da hukumomi suka gudanar, ciki har da ci gaban da shirin “Youth for Peace” (Y4P) da shirin Jakadun Matasan Afirka na AU (AYAPs) suka samu wajen tallafawa kasashe mambobi don inganta ajandar Matasa, Zaman Lafiya da Tsaro (YPS).
Baya ga karfafa hadin gwiwa, musayar bayanai da tsara shirye-shirye tare tsakanin RECs, mahalarta taron sun tattauna kan “yadda za a daidaita tsare-tsaren YPS na RECs da Tsarin Nahiyar (CFYPS), yayin da tsarin ke ci gaba da samun karfi daga Kudirin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2250, wanda ke jaddada muhimmancin matasa a matsayin masu kawo sauyi wajen kiyayewa da inganta zaman lafiya da tsaro”.
Afirka ce ke da yawan al’ummar da suka fi kowace nahiya yawan matasa a duniya. “An kira taron CFYPS ne domin gane muhimmiyar rawar da matasa ke takawa wajen gina zaman lafiya a fadin nahiyar, da kuma karfafa samar da karin tsare-tsaren ayyuka kan batun Matasa, Zaman Lafiya da Tsaro (YPS) daga kasashe mambobi”.
An bayyana kalubalen zaman lafiya da tsaro da ke tasowa a nahiyar a matsayin sauye-sauyen gwamnati ta hanyar da ta saba wa tsarin mulki, tsattsauran ra’ayi mai haifar da tashin hankali, barazanar tsaro da ke da alaka da sauyin yanayi, tashin hankalin da ke tattare da zabe, da kuma karuwar bukatar matasa na samun damar shiga harkokin tafiyar da al’amura yadda ya kamata.
An kuma gabatar da kudirin ECOWAS na karfafa ayyukan YPS da gina zaman lafiya ta hanyar tsarin ta na rigakafin rikici a yayin taron.
Aisha.Yahaya, Lagos



