Wasanni

Arsenal Ta Tsawaita Yarjejeniyar Haɗin Gwiwa Da Emirates Har Zuwa Shekarar 2033.

Kungiyar Arsenal ta tsawaita yarjejeniyar hadin gwiwarta da kamfanin jiragen sama na Emirates har zuwa shekarar 2033, kamar yadda kungiyar ta Premier League ta sanar a ranar Alhamis; hakan na nufin kamfanin zai ci gaba da zama babban mai daukar nauyin kungiyar (ta hanyar sanya sunansa a gaban rigar ‘yan wasa), da kuma daukar nauyin kayan atisaye da kuma mallakar hakkin sanya sunansa a filin wasan kungiyar.

Ba a bayyana cikakkun bayanai game da kudaden yarjejeniyar ba.

Wannan tsawaita yarjejeniya na ci gaba da hadin gwiwar da ta shafe shekaru 20, wadda ta fara a shekarar 2006 lokacin da Arsenal ta koma filin wasa na Emirates Stadium.

Sabunta yarjejeniyar ya zo ne a wani muhimmin lokaci a tarihin kungiyar bayan nasarar da ta samu na lashe gasar Premier League a kakar wasan da ta gabata.

Sabuwar yarjejeniyar za ta tabbatar da ci gaba da gudanar da shirye-shirye da dama, ciki har da gasar Emirates Cup, inda Arsenal za ta karbi bakuncin kungiyar Borussia Dortmund a gasar ta bana a ranar Lahadi da ta gabata.

“Lashe gasar Premier League babban abin alfahari ne a tarihin kungiyarmu, kuma nasara ce ta kowa da ke da alaka da Arsenal,” in ji Babban Jami’in Gudanarwa Richard Garlick a cikin wata sanarwa.

“Kamfanin Emirates ya taka muhimmiyar rawa wajen samun wannan nasara, inda ya tsaya tare da mu a duk tsawon wannan tafiya tare da raba lokuta masu muhimmanci, kalubale, da nasarorin da suka siffanta kungiyarmu a cikin shekaru 20 da suka gabata.”

Arsenal da Emirates, wadanda za su cika shekaru 20 da fara hadin gwiwarsu a mako mai zuwa, za su kuma fitar da wani gajeren fim na talla don murnar muhimman lokuta a cikin wannan dangantaka, wanda zai nuna tsohon dan wasan baya na Arsenal da Jamus, Per Mertesacker.

 

Aisha.Yahaya,  Lagos

 

 

Reuters/Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button