Majalisar Dinkin Duniya Na Neman Karin Kudade Domin Tunkarar Illolin Girgizar Kasa A Venezuela.

Fiye da makonni biyar bayan mummunan girgizar kasa da ta afku a Venezuela, Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa an fadada ayyukan agaji, inda kimanin mutane 200,000 suka samu tallafin gaggawa.
Da yake jawabi a wani taron manema labarai a hedkwatar Majalisar Dinkin Duniya da ke New York, mataimakin kakakin majalisar, Farhan Haq, ya ce ana gudanar da ayyukan agajin ne ta hanyar hadin gwiwa tsakanin majalisar, abokan huldar agaji, al’ummomin yankin, da hukumomin Venezuela.
“Abokan aikinmu daga Ofishin Kula da Ayyukan Agaji (OCHA) sun sanar da mu cewa mutane 200,000 sun samu tallafin agaji da muhimman ayyuka ta hanyar hadin gwiwar majalisar, abokan hulda, al’ummomin yankin, da hukumomi.
“Wannan tallafi ya hada da abinci mai zafi, kula da lafiya, ruwa mai tsafta, matsuguni, da tallafin shari’a da na kula da lafiyar kwakwalwa ga mata, yara, da kuma masu rauni, yayin da iyalai ke fara dogon tsarin sake gina rayuwarsu,” in ji shi.
Haq ya kara da cewa kungiyoyin agaji sun bayar da rahoton fara aikin tantance bukatun da gwamnatin Venezuela da abokan huldar Majalisar Dinkin Duniya ke yi tare, domin tsara shirye-shiryen farfadowa, sake ginawa, da ci gaba a watanni masu zuwa.
“Kasancewar an samu kashi 42 cikin 100 na kudaden da ake bukata don shirin bayar da agaji kaɗai, ana bukatar ci gaba da samun tallafi daga kasashen duniya domin kungiyoyin agaji su ci gaba da taimaka wa al’ummomi a watanni masu zuwa,” in ji Haq.
A daya bangaren kuma, adadin wadanda suka mutu a hukumance sakamakon girgizar kasa biyu da suka afku a yankin arewa-tsakiyar kasar Venezuela a ranar 24 ga watan Yuni ya karu zuwa 6,125, kamar yadda wani rahoto kan sake ginawa da aka fitar a karshen ranar Litinin ya nuna.
KARANTA KUMA: Adadin Wadanda suka mutu a Girgizar Kasan Venezuela ya kai 3,811
Hukumomi sun ce ana ci gaba da tantance gidajen da suka lalace, amma sun yi gargadin cewa dubban gidaje ba su da aminci ko bayan makonni biyar da afkuwar bala’in.
Sabon rahoton, wanda shi ne na farko da ya bayar da sabbin bayanai kan wadanda bala’in ya shafa cikin kwanaki 10, ya nuna karin mutuwar mutane 579, wanda ya sa adadin ya haura daga mutane 5,546 da aka bayar da rahotonsu a ranar 24 ga watan Yuli.
Wadannan sabbin alkaluma sun nuna cewa tasirin bala’in kan rayuwar mutane na ci gaba da karuwa fiye da makonni biyar bayan girgizar kasar.
NAN/Aisha.Yahaya, Lagos



