Fitattun LabaraiNajeriya

Uwargidan Shugaban Kasa Ta Bukaci Matasan Najeriya Su Kara Himma Wajen Aiki Tukuru

Uwargidan Shugaban Kasa Najeriya Oluremi Tinubu ta yi kira ga matasan kasar da su yi kokarin cimma manyan nasarori tare da guje wa gamsuwa da kananan nasarori kawai.

 

Ta bayyana hakan ne yayin da ta karbi bakuncin shugabannin bangaren matasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

 

Ta bukace su da su rungumi dabi’ar kwazo da himma a dukkan fannuka domin samun ci gaba a rayuwa tare da jaddada muhimmancin hakuri gaskiya da kuma aiki tukuru.

 

KARANTA KUMA: Uwargida ta yi kira da a ba da fifiko ga hadin kai maimakon son kai

“Allah yana sane da bukatunmu a koda yaushe kuma wannan shi ne abin da matasa ba su sani ba kullum suna cikin gaggawa. Ina kuma koya muku yadda za ku koyi gamsuwa da abin da kuke da shi maimakon zama masu roko-roko.

 

“Dole ne ku kasance masu irin tunanin tsuntsun ‘Eagle’ (gaggafa). Idan gaggafa ta ga hadari sai ta yi masa dariya tare da neman hanyar da za ta iya tashi a samansa. Wannan shi ne abin da ya kamata ku duka ku yi. Ya kamata ku rika neman hanyarku ta kashin kai ba wai kawai saboda wani yana da abu ba shi ya sa ku ma kuke son samunsa ba” in ji ta.

Madam Tinubu ta yaba wa shugabannin matasa bisa hadin kan da suka nuna wajen karfafa ayyukan siyasar jam’iyyar musamman a matakin tushe.

 

Ta yi kira ga mambobin bangaren matasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da su yi iya bakin kokarinsu wajen daukaka martabar jam’iyyar yayin mu’amalarsu da ‘yan Najeriya musamman dangane da nasarorin da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta samu.

 

Uwargidan Shugaban Kasa ta jaddada cewa a matsayinsu na daya daga cikin bangarorin jam’iyyar mai mulki wadanda ke da nauyin tallata manufar “Renewed Hope Agenda” (Ajandar Sabuwar Bege) ta gwamnatin mai ci ya zama wajibi ga mambobinta da shugabanninta su nuna jajircewa da kuma kyakkyawar sadaukarwa domin gina makoma mai cike da bege.

Daga nan sai ta mika motocin bas guda tara ga shugabannin bangaren matasa na jam’iyyar APC domin saukaka zirga-zirga yayin ayyukan jam’iyya da na hidimtawa al’umma.

 

Shugaban matasan jam’iyyar APC na kasa Dayo Israel ya nuna godiyarshi ga Uwargidan Shugaban Kasa bisa karamcinta inda ya jaddada cewa matasan za su ci gaba da tallata manufofi da tsare-tsaren jam’iyyar gabanin zaben shekarar 2027 da ma bayan hakan.

 

Ya yi alkawarin cewa bangaren matasan zai ci gaba da goyon bayan shirin “Renewed Hope Agenda” (Shirin Sabon Fatan) na Shugaba Bola Tinubu.

 

“Mun kuduri aniyar goyon bayan shirin ‘Renewed Hope Agenda’. Abin da kika yi a yau ya kara mana karfin gwiwa da damar isa ga jama’a ba wai kawai don tara kuri’u ba har ma don inganta rayuwar ‘yan Najeriya” in ji shi.

 

An mika motocin bas din ga shugaban matasan APC na kasa, Dayo Israel; mataimakin shugaban matasan APC na kasa, Jamaludeen Kabir; da sauran shugabannin shiyyoyi, ciki har da na Babban Birnin Tarayya (FCT).

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button