Shugaban Kasar Philippines Ya Amince A Fitar Da Bayanan Harajin Mataimakin Shugaban Kasa Duterte
Shugaban Jamhuriyar Philippines Ferdinand Marcos Jr. ya ba da izinin sakin bayanan harajin Mataimakiyar Shugaba Sara Duterte ga Majalisar Dattawa don amfani da su a shari’ar tsige ta inda take fuskantar zarge-zargen tara dukiya mara tushe yayin da take kan mulki.
“Ana iya buɗe su ta hanyar amfani da su daga ɓangarorin a matsayin wani ɓangare na shaidarsu” in ji mataimakiyar sakatariyar sadarwa ta Shugaban Ƙasa Claire Castro a cikin wani saƙo a ranar Alhamis.
Ofishin Duterte bai amsa buƙatar Reuters nan take ba don yin sharhi. Ta sha musanta duk wani laifi kuma ta bayyana shari’ar tsigewar a matsayin abin da ya shafi siyasa.
An shirya Majalisar Dattawa wacce ke zaman kotun tsigewa za ta ci gaba da shari’ar a ranar 3 ga Agusta.
A ƙarƙashin dokar Philippines Ofishin Haraji na Cikin Gida zai iya fitar da bayanan haraji na sirri ne kawai tare da amincewar shugaban ƙasa.
KARANTA KUMA: Ciniki tsakanin Najeriya da Philippines ya yi tashin gwauron zabi da kashi 700% cikin shekaru uku
Ko da yake Majalisar Dattawa ta gayyaci takardun harajin Duterte, amma ta hana sakin su har sai ta bi ƙa’idodin sirrin masu biyan haraji.
Majalisar Dattawa ta kuma umurci bankuna da Hukumar Yaki da Safarar Kudaden Haram (Anti-Money Laundering Council) da su gabatar da bayanan harkokin kudi masu alaka da Duterte da mijinta.
Ana tuhumar Duterte da laifuka da suka hada da cin zarafin kudaden gwamnati mallakar dukiyar da ba a san tushenta ba, karbar cin hanci, cin hanci da rashawa da kuma yin barazana ga Shugaba Marcos, uwargidansa, da kuma tsohon kakakin Majalisar Wakilai.
Idan aka same ta da laifi hakan zai bukaci goyon bayan akalla mambobi 16 cikin mambobi 24 na Majalisar Dattawa kuma hakan na iya kawo cikas ga shirin Duterte na tsayawa takarar shugabancin kasa a shekarar 2028.
Marcos da Duterte wadanda suka fito daga manyan iyalai masu tasiri a fagen siyasar Philippines sun samu nasara mai yawa a zaben 2022 bayan sun tsaya takara tare a matsayin abokan kawance. Sai dai daga baya kawancen nasu na siyasa ya rushe sakamakon wani babban sabani da ya shiga tsakaninsu.
Reuters/LADAN NASIDI



