Najeriya

Sarkin Timi Na Ede Ya Yi Kira Ga Shugaba Tinubu Da Ya Tabbatar An Gudanar Da Ingantaccen Zabe.

Timi na Ede, Oba Munirudeen Adesola Lawal, ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya tabbatar an gudanar da zaben gwamna mai ‘yanci, adalci, da kuma amincewa a Jihar Osun a ranar 15 ga watan Agusta.

Ya bukaci Shugaban kasar da ya yi amfani da mukaminsa wajen tabbatar da daidaiton dama ga dukkan jam’iyyun siyasa, yana mai cewa dimokuradiyya tana samun ci gaba ne kawai idan an bi ra’ayin jama’a kuma ‘yan kasa suka samu damar zaben shugabannin da suke so ba tare da tsoratarwa ko wani cikas ba.

Oba Lawal ya kuma yi kira da a kaddamar da aikin fadada hanyar Akoda–Baptist High School–Oke Gada da ke Karamar Hukumar Ede ta Kudu a Jihar Osun.

“Ina amfani da wannan dama wajen yin kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya tabbatar an gudanar da zaben gwamna mai ‘yanci, adalci, da amincewa; ya kamata ya bar mutanen Jihar Osun su zabi dan takarar da suke so a ranar 15 ga watan Agusta,” in ji shi.

Sai dai, basaraken ya bayyana cewa kofarsa a bude take ga dukkan jam’iyyun siyasa da masu neman mukamai, yayin da ya bukaci mutanen Ede su fito kwansu da kwarkwatarsu su zabi Gwamna Ademola Adeleke, yana mai cewa, “Za mu yi amfani da kuri’unmu wajen saka wa gwamnatin Adeleke kan manyan ayyukan ci gaba da samar da ababen more rayuwa da ta yi a garin Ede.

“Haka kuma za mu yi amfani da kuri’unmu wajen cike duk wani gibin da aka samu daga sauran kananan hukumomin Jihar Osun. Za mu cike akwatunan zabe har su cika makil; Allah Ya sanya mu a matsayi mai muhimmanci da fifiko,” in ji shi.

KARANTA KUMA: Gwamnan Jihar Osun Ya Yi Alkawarin Gudanar da Zabe Mai Inganci a ranar 15 ga Agusta

An Cika Alkawari – Gwamna

Yayin da yake jawabi ga jama’a a wajen kaddamar da aikin, Gwamna Adeleke ya bayyana cewa hanyar “alkawari ne da aka cika shi,” yana mai jaddada cewa za ta hanzarta ci gaban tsohon garin na Ede.

“Wannan alkawari ne da aka cika, kuma wannan shi ne irin shugabancin da ke shafar zukatan jama’a. Wannan hanya tana da matukar muhimmanci ga Ede; tana hada manyan unguwannin zama, makarantu, da kasuwa, tare da hada su da hanyoyin da ke zuwa manyan biranen Osogbo da Ibadan. “Tsawon lokaci, al’ummarmu sun sha fama da cunkoson ababen hawa da kuma rashin ingantattun hanyoyi a cikin garin. Sai dai tare da wannan hanyar mai layuka biyu, zirga-zirga a cikin Ede za ta kasance cikin sauri da kwanciyar hankali; harkokin kasuwanci a yankunan Akoda, Cottage, da Oke Gada za su bunkasa; dalibai da ma’aikata za su rika isa makarantu da wuraren aikinsu akan lokaci; sannan harkokin dare da tsaro za su inganta sakamakon samar da fitilun hasken rana.

“Wannan wani bangare ne na tsarin gwamnatinmu na farfado da kayayyakin more rayuwa a dukkan yankunan jihar Osun. Abin da muke yi a Osogbo, shi muke yi a Ila, Iwo, Ile Ife, Ilesha, kuma yanzu a Ede,” in ji Gwamnan.

Gwamnan ya yabawa ma’aikatar ayyuka da kuma ‘yan kwangilar da suka yi aiki mai kyau, inda ya ce injiniyoyin sun yi aiki mai inganci daidai gwargwado.

Yayin da yake kaddamar da titin biyu a hukumance, Adeleke ya bayyana fatan cewa jam’iyyar Accord Party za ta yi nasara a zaben.

 

 

Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button