Shugaban Majalisar Dinkin Duniya ya ziyarci Sham A Wata Ziyara Ta Tarihi Bayan Ficewar Assad Daga Karagar Mulki
Ana sa ran Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres, zai ziyarci kasar Syria a ranar Asabar wannan shi ne karo na farko da shugaban Majalisar Dinkin Duniya mai ci zai kai ziyara tun bayan barkewar yakin basasar kasar da ya shafe kusan shekaru 14 wanda ya yi sanadiyyar mutuwar daruruwan dubban mutane tare da tilasta wa miliyoyin mutane barin gidajensu.
Wannan ziyarar wani muhimmin mataki ne a tsarin sauye-sauyen kasar Syria bayan yakin biyo bayan hambarar da tsohon shugaban kasar Bashar al-Assad da sojojin ‘yan tawaye suka yi a karshen shekarar 2024. Cire Assad daga karagar mulki ya kawo karshen rikicin da ya fara a shekarar 2011 tare da samar da gwamnatin rikon kwarya karkashin jagorancin gwamnatin da ke samun goyon bayan kungiyoyin masu ra’ayin Islama.
Bayan faduwar Assad Guterres ya bayyana “karshen mulkin kama-karya a Syria” a matsayin wani ci gaba mai cike da bege ga kasar Sham da ma yankin baki daya.
A yayin ziyararsa ana sa ran Guterres zai tattauna da Shugaba Ahmed al-Sharaa—tsohon shugaban reshen kungiyar al-Qaeda a Sham wanda ya kasance a karkashin takunkuman Majalisar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya dangane da ta’addanci har zuwa watan Nuwambar 2025.
A cewar kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stephane Dujarric, Sakatare-Janar din zai kuma gana da Ministan Harkokin Wajen Syria Asaad al-Shaibani da manyan jami’an gwamnati da kuma wakilan kungiyoyin farar hula na Syria.
Dujarric ya bayyana cewa Guterres zai jaddada cewa yanzu Syria tana da damar “ba wai kawai ta farfado daga rikici ba har ma ta shimfida harsashin makomar da za ta kasance mai kwanciyar hankali mai hada kan kowa, da kuma wadata ga dukkan ‘yan kasar Sham.”
Ana sa ran shugaban na Majalisar Dinkin Duniya zai zauna a Damascus na tsawon kwanaki da dama duk da cewa ofishinsa bai fitar da cikakken tsarin tafiyarsa ba.
Wannan ziyara ta zo ne ‘yan makonni kadan bayan fashewar bama-bamai guda biyu kusa da wani otal a Damascus inda Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kwana lamarin da ya yi tasiri sosai kan ziyarar farko da wani shugaban kasa daga Tarayyar Turai ya kai Syria tun bayan cire Assad daga karagar mulki.
Sham ta Koma Fagen Siyasar Duniya
Gwamnatin Shugaba Ahmed al-Sharaa na kokarin dawo da matsayin Syria a idon duniya da kuma farfado da tattalin arzikinta bayan kusan shekaru 14 na rikici da kuma shekaru da dama na killacewa a karkashin mulkin iyalin Assad.
Sai dai tsarin sauye-sauyen kasar ya fuskanci kalubale masu tsanani ciki har da manyan lamura guda biyu na rikicin bangaranci na addini wadanda suka jarraba alkawuran da Sharaa ya rika yi akai-akai na kare tsiraru masu bin addinai daban-daban a Syria.
KARANTA KUMA: WHO Ta Saki Tallafin Gaggawa na Dala Miliyan 2 ga Lebanon da Iraq da Sham.
A bara an ruwaito cewa kusan Alawites 1,500 – ƙungiyar da Assad ya fito – an kashe su a yankin bakin teku na Syria ta hanyar ƙungiyoyin da ke goyon bayan gwamnati. Watanni bayan haka daruruwan ‘yan tsirarun Druze suma sun rasa rayukansu a lokacin tashin hankali a kudancin Sham.
Guterres ya nuna damuwa game da abubuwan biyu kuma ya yi kira da a hukunta waɗanda ke da alhakin.
Sharaa wanda ya yanke alaƙa da al Qaeda a 2016 ya jagoranci haɗin gwiwar ƙungiyoyin ‘yan tawaye masu tsattsauran ra’ayi waɗanda suka kawar da Assad daga mulki a lokacin wani hari cikin gaggawa a watan Disamba na 2024.
Tun lokacin da ya hau kan mulkin gwamnatinshi ta nemi sake gina dangantakar diflomasiyya ta Sham fiye da abokan hulɗarta na dogon lokaci da Rasha da Iran.
A wani muhimmin ci gaba mai Sharaa ya zama shugaban Syria na farko tun 1967 da ya halarci Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya a New York a bara.
LADAN NASIDI


