Masar Ta Mamaye Gasar Zakarun Matasa Ta ITTF A Afirka

Masar ta lashe kofuna uku cikin hudu na gasar kungiyoyi a gasar matasa ta ITTF ta Afirka ta shekarar 2026, lamarin da ya sake tabbatar da karfinta da kuma yadda ta ke kan gaba a wasan kwallon tebur na matasa a nahiyar Afirka.
An buga wasannin karshe a ranar Laraba a cibiyar wasanni ta Borteyman da ke Accra, Ghana.
Kasar ta Arewacin Afirka ta doke Najeriya, Tunisia, da Algeria domin lashe kofunan matasa ‘yan kasa da shekaru 15 (npjja maza da mata), tare da ci gaba da rike kambun ‘yan kasa da shekaru 19 na mata.
Najeriya, wacce ta zo gasar a matsayin wacce ta lashe kofin a baya, ta fuskanci kalubale mai tsanani kafin ta samu nasara kan kasar da ta karbi bakuncin gasar, wato Ghana, da ci 3-2 a matakin kusa da na karshe.
Sai dai, Masar ta nuna karfi sosai a wasan karshe, inda ta doke Najeriya da ci 3-0 ba tare da ko daya ba.
Ahmed Elsabbagh ne ya fara bude asusun cin kwallaye ta hanyar doke Marvelous Joseph da ci 3-0 (maki 11-8, 11-5, 13-11).
Daga nan, babban dan wasan Masar, Asser Sameh, ya doke Usman Ayoola da ci 3-0 (maki 11-9, 12-10, 11-7).
Hussein Eyad ya kammala nasarar da babbar kwazo ta hanyar doke Samson Joshua da ci 3-0 (maki 11-9, 11-9, 11-8).
Karanta kuma: Masar, Najeriya, da Tunisia Sun Fara Gasar Matasa ta ITTF da Karfi
ITTF na Karfafa Gwiwar Kasashen Afirka su Nemi Karbar Bakuncin Gasar Bayan Nasarar da aka samu a Ghana
A bangaren ‘yan kasa da shekaru 15 na mata, Masar ta doke Tunisia da ci 3-1 domin kwato kambun da ta rasa a hannun Uganda a shekarar 2025.
Har ila yau, ‘yan wasan Masar sun ci gaba da rike kambun ‘yan kasa da shekaru 19 na mata bayan sun doke Algeria da ci 3-0.
Kasancewar ta lashe kofuna uku na kungiyoyi, nasarar da Masar ta samu a Accra ta kara tabbatar da karfinta da kuma yadda ta ke ci gaba da mamaye wasan kwallon tebur na matasa a Afirka.
NAN/Aisha.Yahaya, Lagos



