Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Taya Sabon Firayim Ministan Birtaniya Murna.

 

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya taya Andy Burnham murna bisa karɓar ragamar mulki a matsayin Firayim Ministan Birtaniya.

Shugaban ya sake nanata kudirin Najeriya na karfafa dangantakar dabarun hadin gwiwa da Birtaniya.

A cikin wata sanarwa da kakakin ma’aikatar harkokin waje, Kimiebi Ebienfa, ya fitar, Shugaba Tinubu ya kuma taya gwamnati da al’ummar Birtaniya murna kan abin da ya kira mika mulki cikin lumana, tsari, da sauki, yana mai cewa hakan ya nuna karfin cibiyoyin dimokradiyya da al’adun tsarin mulkin kasar.

Shugaban ya tuna ziyarar aiki da ya kai Birtaniya a watan Maris na 2026, inda ya gudanar da tattaunawa mai amfani da Firayim Ministan da ya gabata.

KARANTA KUMA: Shugaba Tinubu ya taya Badejo-Okusanya murna kan nasarar zaben NBA

Ya bayyana kwarin gwiwar cewa Firayim Minista Burnham zai ci gaba da gina harsashin nasarorin da aka samu a waccan tattaunawa tare da samar da sabbin damammakin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

“Ina fatan binciko sabbin hanyoyin hadin gwiwa da tattaunawa tare da Birtaniya a karkashin sabon Firayim Minista,” in ji Shugaba Tinubu.

Shugaban ya kuma bayyana sha’awarsa ta ganawa da Firayim Minista Burnham da wuri-wuri, ko dai a matakin kasashen biyu ko kuma a tarukan kasa da kasa, musamman a kungiyar Commonwealth, domin zurfafa dangantaka da kuma ciyar da muradun gama-gari gaba.

Ya sake nanata shirye-shiryen Najeriya na yin aiki kafada-da-kafada da sabuwar gwamnatin Birtaniya wajen inganta ci gaban juna da kuma tunkarar kalubalen duniya da ya shafi kowa.

Shugaba Tinubu ya yi wa Firayim Minista Burnham fatan samun nasara a wa’adin mulkinsa tare da tabbatar masa da ci gaba da kudirin Najeriya na karfafa dangantaka mai dorewa tsakanin kasashen biyu.

 

 

Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button