Hukumar INEC Za Ta Yi Wa Masu Ruwa Da Tsaki Bayani Gabanin Zaben 2027

Hukumar Zabe ta Kasa Mai Zaman Kanta (INEC) za ta gudanar da taron manema labarai na duniya da kuma taron masu ruwa da tsaki na kasa a ranar Talata, 6 ga Oktoba, 2026, domin tunawa da cewa saura kwana 100 a gudanar da Babban Zaben 2027.
Hukumar za ta bayar da sabbin bayanai game da shirye-shiryen zaben, ciki har da rajistar masu kada kuri’a, tsarin tsayar da ‘yan takara, harkokin dabaru da kayan aiki, da kuma muhimman matakan tabbatar da inganci da amincin tsarin zaben.
A cikin sanarwar da Babban Sakataren Yada Labarai na Shugaban INEC, Adedayo Aketola, ya fitar, an bayyana cewa Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan (SAN), ne zai yi jawabi a taron, tare da sauran muhimman masu ruwa da tsaki da ke da hannu a tsarin zaben.
Wannan taron na masu ruwa da tsaki na kasa yana nuna kudurin hukumar na tabbatar da cikakken bayyana gaskiya, sadarwa mai inganci da jama’a, da kuma hadin gwiwa tare da muhimman bangarori masu tasiri a fannin zabe.
KARANTA KUMA: INEC ta horar da Jami’an Harkokin Jama’a kan Adana Bayanai da Takardu
Taron zai hada shugabannin jam’iyyun siyasa, hukumomin tsaro da ke karkashin Kwamitin Tuntuɓa na Hukumomin Tsaro kan Tsaron Zabe (ICCES), wakilan kasashen waje (diplomats), abokan hulda na ci gaba, kungiyoyin farar hula, kungiyoyin sa ido kan zabe, masu fafutukar kare hakkin masu nakasa, shugabannin addini da na gargajiya, kungiyoyin matasa, da shugabannin kafofin yada labarai.
Za a gudanar da taron ne a Cibiyar Taro ta Duniya ta Bola Ahmed Tinubu (Bola Ahmed Tinubu International Conference Centre) da ke Abuja.
INEC/Aisha.Yahaya, Lagos



