Indonesiya Ta Tabbatar Da Mutuwar Mutane 10 Tare Da Bacewar Wasu 125 Bayan Wani Jirgin Ruwa Ya Kife

Hukumar ceto ta kasar Indonesia ta bayyana cewa tana ci gaba da neman mutane 125 da suka bace bayan wani jirgin ruwa mai daukar fasinjoji ya kife a Tekun Java tsakanin tsibiran Java da Borneo inda aka tabbatar da mutuwar mutane 10.
Hukumar ta ce masu nutsewa cikin ruwa sun ciro gawa daya daga cikin jirgin a ranar Lahadi bayan da aka ciro gawa uku a ranar Juma’a.
Ta ce “mutane 108 ne suka tsira daga hatsarin.”
Wani jami’in hukumar ceton Putu Sudayana ya ce za a tura wata na’ura mai tafiya karkashin ruwa wadda ake sarrafawa daga nesa a ranar Litinin domin taimaka wa masu nutsewa wajen bincike a cikin jirgin.
Ya ce karfin igiyar ruwa ya kawo cikas ga aikin na ranar Lahadi.
“Ana fatan yanayi a wurin zai yi kyau domin a samu damar fitar da sauran wadanda hatsarin ya shafa da ke makale a cikin jirgin” in ji Sudayana.
Hukumar ta tsawaita wa’adin aikin ceto da mako guda saboda yawan mutanen da suka bace da kuma lokacin da ake sa ran zai dauka wajen ciro jirgin da kuma mayar da shi yadda ya kamata.
Jirgin ruwan mai daukar fasinjoji mai suna Virgo Transport 8 yana dauke da mutane 243 ne ciki har da ma’aikatan jirgin 30 lokacin da ya kife sakamakon mummunan yanayi a ranar 13 ga watan Satumba.
Jirgin yana kan hanyarsa ne daga Surabaya a Gabashin Java zuwa Banjarmasin a Kudancin Kalimantan tafiyar da za ta dauki sa’o’i 20.



