Shugaban kasar Zambia Ya Sake Lashe Zabe Domin Wa’adi Na Biyu

Hukumar zaben Zambia ta sanar da cewa an sake zaben Shugaba Hakainde Hichilema domin wa’adi na biyu na shekaru biyar bayan ya samu kashi 60 cikin dari na jimillar kuri’un da aka kada.
An yi tsammanin nasarar Hichilema inda babban abokin hamayyarsa Brian Mundubile ya samu kashi 38 cikin dari na kuri’un da aka kada sauran ‘yan takara 12 kuwa sun yi nisa sosai a baya.
Sakamakon ya zo ne bayan wani tsari mai cike da takaddama inda Mundubile mai shekaru 55 ya fara ikirarin samun nasara tare da zargin cewa an samu matsaloli ko magudi a yayin zaben duk da cewa bai gabatar da hujjoji ba.

Haka kuma lamarin ya biyo bayan kama wasu manyan ‘yan adawa a wani samame da aka kai ranar Juma’a inda hukumomi suka zarge su da shirin tayar da tarzoma. Mundubile ya bayyana zargin a matsayin karya.
KARANTA KUMA:
A cikin wata sanarwa bayan an bayyana shi a matsayin wanda ya yi nasara Hichilema mai shekaru 64 ya ce “Mun ji matukar godiya da tawali’u bisa amincewar da kuka nuna mana.”
Ya ce zaben ya nuna cewa Zambia kasa ce mai zaman lafiya, bin doka da oda, tare da kasancewa “kasa mai tsarin dimokradiyya da ke warware sabanin ra’ayi ta hanyar kada kuri’a, ba ta wata hanya ta daban ba.”
“Ga ‘yan kasa da suka fi goyon bayan ra’ayoyin da abokan hamayyarmu suka gabatar mun ji ku, kuma za mu ci gaba da yi muku aiki” in ji shi.
Daruruwan magoya bayan Hichilema, wadanda suka sanya tufafi masu launin ja na jam’iyyarshi ta United Party for National Development (UPND) sun cika titunan babban birnin kasar Lusaka domin yin murna bayan sanar da sakamakon zaben.
BBC/LADAN NASIDI



