
An zabi Najeriya a matsayin memba na Majalisar Kare Hakkin Dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya a wa’adin 2027-2029 bayan ta samu kuri’u 172 daga cikin 181 a zaben da aka gudanar a ranar Talata 13 ga Oktoba 2026.
Ma’aikatar Harkokin Waje ta bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ta fitar an Abuja kuma mai magana da yawunta Oluwafemi Adeniyi ya sanya wa hannu.
An zabi Najeriya tare da wasu kasashe 14 don yin wa’adi na shekaru uku daga 1 ga Janairu 2027 zuwa 31 ga Disamba 2029.
KARANTA KUMA:http://Shugaba Tinubu Ya Sake Kira ga Gyaran Majalisar Tsaro ta Majalisar Dinkin Duniya
A cewar ma’aikatar zaben ya nuna amincewar kasashen duniya ga kudurin Najeriya na inganta da kare hakkin dan adam a duk duniya.
“Gwamnatin Tarayya ta Najeriya ta bayyana godiyarta ga kasashen mambobin Majalisar Dinkin Duniya saboda goyon bayansu ga takarar Najeriya” in ji sanarwar.
Ma’aikatar ta bayyana cewa Najeriya za ta ci gaba da inganta tattaunawa hadin guiwa da girmama juna tsakanin kasashe mambobin yayin da take aiki tare da sauran membobin Majalisar don inganta kare hakkin dan adam.
Haka kuma ta sake jaddada kudurin ƙasar na yin aiki tare da ɓangarori daban-daban da kuma shirye-shiryen da ke kare mutuncin ɗan adam adalci da ‘yancin ɗan adam.
Kwamitin Kare Haƙƙin Dan Adam na Majalisar Ɗinkin Duniya mai membobi 47 yana da alhakin haɓaka da kare haƙƙin ɗan adam a duk duniya.



