Najeriya

Shugaban Najeriya Ya Rusa Kwamitin Shugaban Kasa Kan Kadarorin Gwamnatin Tarayya.

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da rusa Kwamitin Shugaban Kasa mai kula da aiwatar da batun rarraba kadarorin Gwamnatin Tarayya (PIC) nan take, lamarin da ya kawo karshen aikin kwamitin bayan ya shafe shekaru 26 yana gudanar da ayyukansa.

An sanar da wannan mataki ne a cikin wata sanarwa da mai bai wa Shugaban Kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis da ta gabata.

A cewar mai bai wa Shugaban Kasa shawarar, daga yanzu, Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Prince Lateef Fagbemi, ne zai rika kula da dukkan batutuwan da suka shafi ayyukan kwamitin da aka rushe din.

Fadar Shugaban Kasa ta bayyana cewa, kwamitin ya fara wuce iyakar aikin da aka dora masa tun farko, lamarin da ya haifar da shari’o’i da dama a sassan kasar nan, har ta kai ga ba a sake ganin bukatar ci gaba da kasancewarsa ba.

KARANTA KUMA: Tawagar Sadarwa ta Gabatar wa Shugaba Tinubu Bayani kan Tasirin Shirin ‘Renewed Hope’

Saboda haka, Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a mika dukkan nauyin da ya rataya a wuyan kwamitin — wanda aka dade ana aiki da shi tun kafin ranar 5 ga watan Nuwamba, 2025 — ga Babban Lauyan Tarayya, tare da fara aiwatar da hakan nan take.

Har ila yau, Shugaban Kasa ya umurci tsohon Sakataren kwamitin, B. S. Dutsin-Ma, da ya daina gudanar da duk wani aiki a madadin kwamitin da aka rushe ko kuma a madadin Gwamnatin Tarayya dangane da tsoffin ayyukan kwamitin nan take.

An kafa kwamitin ne a shekarar 2000 a karkashin gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo domin kula da batun mayar da kadarorin kasa zuwa hannun masu zaman kansu, sayarwa, da kuma bayar da su haya, a matsayin wani bangare na manufar gwamnati ta mayar da kadarori zuwa kudi.

Kwamitin ya kunshi wakilai daga muhimman ma’aikatun gwamnati, ciki har da na Gidaje, Sufuri, Shari’a, Lafiya, da Noma, tare da rundunar ‘yan sandan Najeriya, inda aka zabo mambobinsa daga bangarorin gwamnati da na masu zaman kansu.

Onanuga ya tunatar da cewa, Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) ta amince da kafa kwamitin bincike a ranar 22 ga watan Maris na shekarar 2001, domin samar da takardar matsayar gwamnati (White Paper) da za ta zama jagora wajen aiwatar da shawarwarin da kwamitin zai bayar bayan kammala aikinsa na tsawon watanni 21.

 

 

Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button