Afirka

Majalisar Dinkin Duniya Ta Nada Ivanko Domin Ya Kula Da Tsarin Kawo Karshen Ayyukan Tawagarta A Yammacin Sahara

Majalisar Dinkin Duniya ta nada Alexander Ivanko domin ya kula da aikin rufe ayyukan tawagarta a yankin Western Sahara wato MINURSO bayan da Kwamitin Tsaro ya gaza sabunta wa’adin aikin tawagar wanda ya kare a ranar 31 ga watan Oktoba.

Kakakin Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Stéphane Dujarric ya bayyana cewa Sakatare Janar António Guterres ne ya nada Ivanko wanda a baya ya kasance Wakilin Musamman na Sakatare Janar a Western Sahara domin ya jagoranci wannan tsari.

Yayin wani taron manema labarai na yau da kullum Dujarric ya ce Ivanko “zai yi aiki tare da karamar tawaga karkashin jagoranci da kulawar Ofishin Tallafawa Ayyuka na Majalisar Dinkin Duniya.”

Dujarric ya kara da cewa, tawagar za ta kula da tsarin dawo da masu sanya ido na soja zuwa kasashensu da kuma mika kadarori da kayan aikin da suka mallaki kasashen da suka bayar da gudummawar sojoji tare da tabbatar da cewa an yi amfani da kayayyaki da kadarorin da suka mallaki Majalisar Dinkin Duniya yadda ya kamata.

Guterres ya yi kira ga dukkan bangarorin da abin ya shafa da su “Ba da cikakken hadin kai domin tabbatar da cewa an kammala aikin rufe tawagar cikin aminci tsari da kuma cikin sauri.”

KARANTA KUMA: Kwamitin Tsaro Na Majalisar Dinkin Duniya Ya Kawo Karshen Aikin Wanzar Da Zaman Lafiya Na Shekaru 35 A Western Sahara

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar 1 ga watan Nuwamba Sakatare Janar din ya jaddada cewa ficewar tawagar MINURSO ba za ta shafi hakkokin al’ummar Western Sahara ba.

Guterres ya bayyana cewa ficewar tawagar “Ba ya soke hakkokin al’ummar Western Sahara da ba za a iya kwace musu ba ciki har da hakkin yanke makomarsu da kansu.”

Ya yi kira ga dukkan bangarorin da su “Girmama tare da kare wadannan hakkoki” yayin da ya nuna damuwa game da yanayin tsaro da kuma yiwuwar sake barkewar rikici.

Babban jami’in Majalisar Dinkin Duniya ya kuma yi kira ga wadanda abin ya shafa da su “Yi taka tsantsan sosai kuma su guji ayyukan da ke kara tashin hankali ko kuma su kawo cikas ga zaman lafiyar yankin.”

Ya sake jaddada kudirin Majalisar Dinkin Duniya na tallafawa tattaunawa da kokarin cimma mafita ta siyasa mai adalci mai dorewa kuma wacce aka amince da ita ta hannun Wakilinsa na Yammacin Sahara Staffan de Mistura.

Guterres ya kuma yaba da gudummawar da MINURSO ta bayar tun lokacin da aka kafa ta a shekarar 1991 musamman wajen sa ido kan tsagaita wuta da kuma tallafawa kokarin cimma matsaya ta siyasa.

Ya yaba wa shugabancin Ivanko a lokacin bayan sake barkewar rikici a shekarar 2020.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button