Siyasa

Gwamnan Jihar Ekiti Ya Fara Wa’adi Na Biyu A Ofis

An rantsar da Gwamnan Jihar Ekiti Biodun Oyebanji domin wa’adi na biyu inda ya zama gwamna na farko da ya yi wa’adi biyu a jere tun lokacin da aka kafa jihar a shekarar 1996.

Ya karbi rantsuwar ofis da misalin karfe 12:32 na GMT a dandalin Ekiti Parapo inda aka gudanar da bikin rantsarwar.

Babban Alkalin Jihar Ekiti Mai Shari’a Adekanye Ogunmoye ne ya jagoranci karbar rantsuwar daga hannun Gwamnan wanda ya samu rakiyar matarsa Farfesa Olayemi Oyebanji wato Uwargidan Gwamnan Jihar Ekiti.

KARANTA KUMA:http://Mataimakin Shugaban Kasa Shettima Ya Isa Ekiti Domin Bikin Rantsar da Gwamna Oyebanji

Kafin rantsar da Gwamnan an rantsar da mataimakiyarsa Mrs. Monisade Afuye wacce ita ma ta karbi rantsuwar ofis domin wa’adi na biyu.

An fara zaben Oyebanji da Afuye a matsayin gwamna da mataimakiyar gwamna a shekarar 2022.

An sake zaben su a ranar 20 ga watan Yuni 2026 inda Oyebanji ya samu kuri’u 319,224 wanda hakan ya ba shi damar ci gaba da rike mukamin na wani wa’adin.

Ana sa ran wa’adi na biyu na gwamnan zai kare ne a shekarar 2030.

Tun bayan kafa Jihar Ekiti a shekarar 1996 babu wani Gwamna da ya taba yin wa’adi biyu a jere kafin Oyebanji.

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ne ya wakilci Shugaba Bola Ahmed Tinubu a wajen bikin, inda ya halarci taron a matsayin Babban Bako na Musamman.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button