
Sarki Felipe na VI na Spain ya yi kira da a karfafa dangantaka da Morocco a lokacin wata ziyara mai muhimmanci da ya kai Ceuta inda ya sake tabbatar da ikon Spain kan yankin Arewacin Afirka a yayin da ake ci gaba da rikici kan ƙaura da kuma kula da kan iyaka.
Sarkin tare da rakiyar Sarauniya Letizia ya ce ikon Spain kan Ceuta da Melilla ba za a iya yin shawarwari ba yayin da ya jaddada bukatar hadin gwiwa da kyakkyawar dangantaka tsakanin makwabtaka da Morocco.
Ziyarar ita ce ta farko da sarkin Spain ya kai Ceuta tun 2007 kuma ta zo ne a daidai lokacin da dangantaka ke tsami kan ƙaura inda yankunan biyu suka ci gaba da zama tushen rashin jituwa tsakanin Madrid da Rabat.
KARANTA KUMA: Sabon Jakadan Najeriya na Neman Ƙarfin Hulɗa da Spain
An ruwaito cewa ‘yan cirani sama da 70,000 sun shiga Ceuta a ranakun 30 da 31 ga Yuli a lokacin kwararar bakin haure da ba a taɓa gani ba. An mayar da mutane da yawa zuwa Morocco cikin sa’o’i yayin da wasu kuma suka ci gaba da kasancewa cikin mawuyacin hali suna kwana a kan tituna da rairayin bakin teku.
Matsalar ƙaura ta kuma haifar da muhawarar siyasa a Spain kafin babban zaɓen da aka shirya yi a ranar 29 ga Nuwamba inda wasu ‘yan siyasa na adawa suka zargi Morocco da amfani da ƙaura don matsa lamba kan siyasa. Morocco da Firayim Ministan Spain Pedro Sánchez sun yi watsi da zarge-zargen.
Sarki Mohammed na VI na Morocco ya soki abin da ya kira kalaman siyasa da kafofin watsa labarai marasa da’a da ke amfani da rikicin yana mai dage cewa bai kamata a yi wa hadin gwiwa da Spain matsin lamba ko cin zarafi ba.
A lokacin ziyarar ma’auratan masarautar Spain sun kuma yi wa bakin haure da suka mutu a wani makabarta da ke kokarin isa Ceuta ciki har da wadanda suka nutse yayin da suke kokarin yin iyo a kan shingen kan iyaka.
Ceuta wacce ke gabar tekun Arewacin Afirka babbar hanyar shiga ga bakin haure da ke neman isa Turai.
Rikicin ya sake sabunta damuwa game da illolin hijira ba bisa ka’ida ba da kuma bukatar hanyoyin aminci ingantattun hanyoyin neman mafaka da kuma kariya ga bakin haure masu rauni.
Duk da ci gaba da rashin jituwa kan ‘yancin kai da kula da kan iyaka Spain da Morocco suna ci gaba da hadin gwiwa kan hijira da sauran batutuwan da suka shafi kasashen biyu.
Afrikanews/Aisha.Yahaya, Lagos



