Jakadun ECOWAS A Majalisar Dinkin Duniya Sun Zabi Sabon Shugaba

Kungiyar Jakadun ECOWAS a Majalisar Dinkin Duniya ta zabi sabon Shugaba a birnin New York bayan kammala taronta na wata-wata na takwas na shekarar 2026.
Sabon Shugaban Jakada Coly Seck shi ne wakilin dindindin na kasar Senegal a Majalisar Dinkin Duniya.
An gudanar da taron ne a ofishin wakilcin dindindin na kasar Saliyo a Majalisar Dinkin Duniya karkashin jagorancin tawagar masu sa ido ta dindindin ta ECOWAS a Majalisar.
Kungiyar ta tattauna batutuwan da suka shafi siyasa da tattalin arziki a yankin tare da samun bayanai game da tattaunawa da sakamakon taron kolin shugabannin kasashen ECOWAS karo na 69 da aka gudanar a kasar Saliyo.
KARANTA KUMA: ECOWAS ta sake jaddada kudirinta na bunkasa masana’antu a yankin
Haka kuma taron ya samu sabbin bayanai kan batutuwan da ake tattaunawa a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya dangane da zaman lafiya da tsaron kasa da kasa da kuma shirin kungiyar na taron Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) karo na 81 mai zuwa da kuma matsayar kungiyar game da goyon bayan ‘yan takara don mukamai a hukumomin kasa da kasa.
An kammala taron da bikin mika ragamar shugabancin kungiyar inda aka yaba wa wakilin dindindin na Saliyo a Majalisar Dinkin Duniya kuma tsohon shugaban kungiyar Jakada Michael Imran Kanu saboda jagorancinsa na misali da kuma gudummawar da ya bayar wajen cimma manufofin kungiyar da ayyukanta na hadin gwiwa a Majalisar Dinkin Duniya.
Sabon Shugaba wanda kuma shi ne wakilin dindindin na Senegal a Majalisar Dinkin Duniya Jakada Coly Seck ya bayyana godiyarshi ga tawagar masu sa ido ta dindindin ta kungiyar ECOWAS a Majalisar Dinkin Duniya saboda gagarumar goyon baya da kuma hadin gwiwar da suka bayar wajen gudanar da ayyukan kungiyar a Majalisar.
Ladan Nasidi.



