Tawagar Tarayyar Turai Ta Ziyarci Wurin Ajiye Kayan Aiki Na ECOWAS A Saliyo.

Wakilan Tarayyar Turai (EU) da ƙasashen da ke cikin Tarayyar Turai sun ziyarci Tashar Kula da Kayayyakin ECOWAS da ke Lungi Saliyo domin su fahimci wuraren aiki rawar da take takawa da kuma wurin da take a cikin tsarin zaman lafiya da tsaro na yankin.
An kuma yi wannan ziyara ne don ƙara fahimtar tawagar game da manufar da ayyukan tashar da aka ɗora kwanan nan a cewar wata sanarwa a shafin yanar gizon ECOWAS.
Kwamandan Tashar Kula da Kayayyakin ECOWAS Kyaftin Navy I. J. Akpa ya karɓi tawagar EU wanda ya yi wa baƙi bayani game da “wajabcin kayan aiki da kuma rawar da take takawa wajen gudanar da Tashar a matsayin ikon jigilar kayayyaki na yankin ECOWAS wanda ke tallafawa ayyukan zaman lafiya taimakon jin kai amsawar gaggawa da sauran buƙatun yanki da aka wajabta“.
KARANTA KUMA: http://EU da EIB Sun Bayyana Karuwar Kasirin Shirin Karfafa Africa ga ‘yan kasuwa.
Akpa ya bayyana cewa taron ya ba da damar fayyace manufa da ayyukan wannan cibiyar ajiya da rarraba kayayyaki (ma’ajiya) tare da inganta fahimtar rawar da take takawa a tsarin samar da kayayyaki da dabaru na yankin ECOWAS.
Daga nan wakilan Tarayyar Turai (EU) sun zagaya wurare na 1 da na 2 na cibiyar inda suka duba sassan gudanarwa wuraren ajiye kaya wuraren zama da sauran kayan aiki da wuraren tallafawa ayyuka.
Tawagar ta bayyana “gamsuwa da kayan aikin da ke wurin tare da nuna cewa ziyarar ta ba su damar fahimtar ainihin manufa karfin aiki da kuma amfanin da ake sa ran cibiyar ajiye kayayyaki ta ECOWAS za ta samar”.
Wannan ziyarar wani bangare ne na ci gaba da hulda tsakanin cibiyar da abokan hulda na yanki da na kasa da kasa tun bayan kaddamar da ita a ranar 18 ga watan Yulin 2026 yayin da take ci gaba da bunkasa rawar da take takawa a matsayin muhimmiyar cibiyar samar da kayayyaki da dabaru ga ECOWAS.
Tawagar ta EU ta kunshi Emilio Rossetti Mukaddashin Shugaban Tawagar Tarayyar Turai Olivier Huot Mukaddashin Jakadan Faransa Irene Toeller Mukaddashin Jakadan Jamus da Charlie Suilen Mai Ba da Shawara kan Tsaron Yanki a Tawagar EU.
Tawagar ta samu rakiyar Funsho Ibrahim Mai Ba da Shawara kan Harkokin Siyasa a Ofishin Wakilin ECOWAS da Joe Skeff Manajan Darakta na kamfanin bada kariya na PROTEC Security Services.



