Kenya Ta Tabbatar Da Rashin Samun Sabon Bullar Cutar Ebola Bayan Gudanar Da Gwanje – Gwaje 293

Ma’aikatar Lafiya ta Kenya ta sanar a ranar Lahadi da ta gabata cewa kasar ba ta sake samun wani sabon bullar cutar Ebola ba bayan gudanar da gwaje-gwaje guda 293 tun bayan mutuwar wani mutum da aka tabbatar yana dauke da cutar a ranar 5 ga watan Oktoba.
Kasar ta tabbatar da bullar cutar Ebola a karon farko (wadda aka shigo da ita daga waje) a ranar 6 ga watan Oktoba, bayan da wani dan kasa ya mutu sakamakon cutar a birnin Nairobi babban birnin Kenya bayan ya dawo daga Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo.
Ma’aikatar Lafiyar ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa an gudanar da gwaje-gwaje kan samfurori 293 da aka samu daga rahotanni ko sanarwa guda 289, kuma mutum daya ne kawai aka tabbatar yana dauke da cutar.
KARANTA KUMA: Najeriya ta kara sa ido kan cutar Ebola bayan bullarta a Kenya
Bugu da kari mutane 108 daga cikin 122 da aka gano sun yi mu’amala da wanda ya fara kamuwa da cutar suna cikin killacewa, kuma ba su nuna alamun cutar ba tukuna.
Ma’aikatar ta yi kira ga jama’a da su kwantar da hankalinsu tare da ci gaba da kasancewa cikin shiri da sa ido sannan ta bukaci duk wanda ke da fargabar cewa ya iya kamuwa da cutar ko kuma yake nuna alamunta da ya nemi kulawar likita.
Kenya ce kasa ta hudu da ta samu bullar cutar da ke da alaka da annobar Ebola a gabashin Congo—annoba ta biyu mafi girma a tarihi da ta shafi mutane sama da 8,000.
Reuters/Aisha.Yahaya, Lagos



