Najeriya
Shugaba Tinubu Ya Gana Da Aliko Dangote A Legas

Shugaba Tinubu ya gana da shugaba kuma babban jami’in gudanarwa na kamfanin Dangote Group Aliko Dangote ranar Juma’a a gidansa da ke unguwar Ikoyi a birnin Lagos.
Wannan ganawa ta zo ne kwanaki kadan bayan da kamfanin Dangote Group ya ci gaba da aiwatar da manyan tsare-tsaren zuba jari wadanda suka hada da fadada matatar man fetur dinsa da ke Legas da kuma kaddamar da sabon aikin matatar mai na dala biliyan 16 a kasar Kenya matakan da ke nuna karuwar rawar da kamfanin ke takawa a bangaren makamashi da masana’antu na Najeriya da ma nahiyar Afirka baki daya.



