Najeriya

Akwa Ibom: Shugaba Tinubu Ya Ƙaddamar Da Filin Jiragen Sama A Uyo

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da sabon sashen tashi da saukar jiragen sama a Filin Jirgin Sama na Duniya na Victor Attah da ke Uyo a Jihar Akwa Ibom matakin da ke nuna fara gudanar da zirga-zirgar jiragen sama na kasa da kasa a wurin.

Shugaban ya kaddamar da wurin ne a ranar Juma’a yayin ziyarar aiki da ya kai Jihar Akwa Ibom inda kuma ya yaba wa Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio sannan ake sa ran zai halarci taron yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Yayin da yake tuno dangantakarsa ta dadewa da Jihar Akwa Ibom Shugaba Tinubu ya bayyana ziyarar a matsayin komawa gida inda ya tuna ayyukan da ya gudanar a jihar kafin ya hau babban mukamin siyasa na kasar.

“A gare ni wannan tamkar komawa gida ne. Na taba zama a nan Akwa Ibom a matsayin mai duba lissafin kudi a kamfanin Mobil. Mun gina Ibeno, muka bunkasa Eket kuma muka yi duk abin da ya kamata mu yi. Ban taba yin mafarkin cewa zan zama shugaban kasa har in kaddamar da filin jirgin sama da aka sanya wa sunan tsohon abokin aikina Gwamna Victor Attah ba” in ji Shugaban.

Tun da farko Shugaba Tinubu ya isa Uyo babban birnin Jihar Akwa Ibom tare da rakiyar Uwargidan Shugaban Kasa Sanata Oluremi Tinubu, domin gudanar da wannan ziyara ta hukuma.

Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima tare da matarsa ​​Nana Shettima da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio da Gwamnan Jihar Akwa Ibom Umo Eno da sauran manyan jami’ai sun tarbi Shugaban Kasa da Uwargidan Shugaban Kasa.

Shugaba Tinubu ya kuma yaba wa Gwamnan Jihar Akwa Ibom Umo Eno bisa hangen nesa da ya nuna wajen jagoranci da kuma kudirinsa na kammala aikin filin jirgin saman inda ya bayyana cewa ya amince da bukatar fara gudanar da zirga-zirgar jiragen sama na kasa da kasa a filin jirgin ba tare da bata lokaci ba bayan samun takardar bukatar a hukumance.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button