Shugaba Tinubu Ya Taya Tawagar Najeriya Murnar Nasarar Da Ta Samu A Gasar Commonwealth

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya tawagar ‘yan wasan Najeriya murna bisa bajintar da suka nuna a gasar Commonwealth da aka gudanar a Glasgow Scotland.
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai da dabaru Mista Bayo Onanuga ya sanya wa hannu Shugaban ya yaba wa ‘yan wasan bisa nuna juriya da kuduri da da’a da kuma kwarewa da halayen da suka zama alamar dabi’ar ‘yan Najeriya.
Haka kuma Shugaba Tinubu ya yaba wa tawagar Najeriya bisa daga tutar kasar tare da nuna girma da alfahari inda ya jaddada cewa lambobin yabo guda 24 da suka samu wato zinare 10 da azurfa 7 da tagulla 7 kuma shaida ce ta kwazon da suka yi da kuma juriyarsu.
KARANTA KUMA: Shugaba Tinubu ya taya NIPR murna bisa samun karbuwa a matakin duniya
Shugaban ya bayyana cewa kwarewar da kowane dan wasa ya samu za ta zama ginshiki mai karfi na samun manyan nasarori a gasannin kasa da kasa na gaba tare da zaburar da matasan Najeriya da dama su rungumi dabi’un sadaukarwa da kuma hidimtawa kasa.
Shugaba Tinubu ya yaba wa shugabancin Kwamitin Wasannin Olympics na Najeriya da Hukumar Wasanni ta Kasa bisa ci gaba da nuna jajircewa wajen bunkasa harkokin wasanni da kuma goyon bayan ‘yan wasa.
Shugaban ya bukaci ‘yan wasan da su ci gaba da mai da hankali tare da neman cimma kololuwar nasara.
Ya ce: “Ko ta hanyar hawa matakin karɓar lambobin yabo ko kuma ta hanyar nuna bajinta da jaruntaka a gasar kowane memba na tawagar Najeriya ya wakilci ƙasarmu cikin mutunci da girma da alfahari.”
“A madadin gwamnatin Najeriya, ina miƙa godiya ta musamman ga ‘yan wasanmu masu horarwa da jami’an fasaha da ma’aikatan lafiya masu gudanarwa da duk waɗanda sadaukarwarsu ta sa aka samu damar shiga gasar.”
Shugaba Tinubu ya sake nanata cewa gwamnatinsa ta tsaya tsayin daka wajen saka hannun jari don bunkasa harkokin wasanni da ƙarfafa hukumomin wasanni da inganta wuraren horarwa da kuma samar da ƙarin damammaki ga ƙwararrun ‘yan wasan Najeriya domin su yi fice a matakin nahiya da na duniya baki ɗaya.
LADAN NASIDI



