Wasanni

Shugaban CAF Motsepe Ya Isa Abuja Domin Halartar Babban Taron CAF Na 48

Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) Dr. Patrice Motsepe ya isa babban birnin tarayyar Najeriya Abuja a ranar Laraba inda aka tarbe shi cikin yanayi na nuna farin ciki sosai gabanin taron babban zauren CAF karo na 48 da za a gudanar a ranar Asabar.

A lokacin da ya sauka a sashen shugabanni na filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe Shugaba Motsepe ya samu tarba daga Shugaban Hukumar Wasanni ta Kasa Mallam Shehu Dikko da Mashawarcin Musamman ga Dr. Motsepe kuma tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya (NFF) Amaju Melvin Pinnick da Sakatare Janar na CAF Mista Samson Adamu da Shugaban Ayyuka na CAF (Project Lead) wanda ke kula da shirye-shiryen OGA da kuma Kyaututtukan CAF Dr. Christian Emeruwa; da Shugaban Ayyuka na Najeriya (Project Lead) na wadannan taruka Dr. Ademola Olajire tare da sauran manyan jami’ai da ma’aikatan CAF.

Jirgin sa na alfarma ya sauka a filin jirgin da misalin karfe 5:51 na yamma kuma nan take tawagarsa ta wuce zuwa otal din Transcorp Hilton, inda dukkan manyan baki (VVIPs) wakilai jami’ai da ma’aikatan CAF baki da aka gayyata da sauran masu ruwa da tsaki suka sauka domin taron babban zauren na ranar Asabar.

KARANTA  KUMA: Kyaututtukan CAF na 2026: Ana Ci Gaba da Kada Kuri’a Gabanin Bikin

Wannan shi ne karo na farko cikin shekaru 17 da Najeriya za ta karbi bakuncin taron babban zauren CAF wanda shi ne babban taro na masu gudanar da harkokin kwallon kafa da masu ruwa da tsaki a nahiyar Afirka. Taron yana hada shugabanni da masu gudanarwa na Hukumar Kwallon Kafa ta Afirka (CAF) mambobin kwamitin zartarwa na CAF shugabanni da sakatarorin kungiyoyin kwallon kafa na kasashe 54 mambobin CAF baki na musamman daga hukumar FIFA ciki har da Shugaban FIFA da Sakatare Janarbaki daga sauran tarayyar kwallon kafa na duniya da sauran masu ruwa da tsaki a wasan a matakin duniya.

Haka kuma wannan shekarar ita ce karo na farko da kasa daya za ta karbi bakuncin taron babban zaure da kuma bikin bayar da kyaututtukan CAF a lokaci guda. Bikin kyaututtukan CAF shi ne babban taron karrama mutane a fannin kwallon kafa a Afirka, wanda ke hada fitattun ‘yan wasa da masu ruwa da tsaki na baya (tsoffin gwaraza) da na yanzu tare da manyan jami’an CAF baki da sauran masu ruwa da tsaki. Za a gudanar da bikin bayar da kyaututtukan CAF a birnin Legas a ranar Laraba 2 ga watan Disamba.

Yayin da aka tsara gudanar da Babban Taro na Musamman (OGA) a Cibiyar Taro ta Duniya ta Bola Ahmed Tinubu za a gudanar da bikin bayar da kyaututtuka na CAF a cikin babban ginin Cibiyar Al’adu da Fasaha ta Wole Soyinka wanda a da aka fi sani da National Theatre.

Rarraba takardun shiga (accreditation) don Babban Taro na CAF zai fara ne a ranar Alhamis.

Babban Taro na 48 na CAF (OGA) zai gudana ne a ranar Asabar 21 ga watan Nuwamba 2026 an Abuja Najeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button