Duniya

Amurka Da Denmark Sun Cimma Yarjejeniya Kan Kasancewar Sojojin Amurka A Greenland.

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Amurka Denmark da Greenland sun cimma yarjejeniyar da za ta bai wa Washington damar fadada kasancewar sojojinta a tsibirin, tare da hana abokan gāban Amurka kafa sansanonin soji a wurin.

Ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a ta hanyar wani sako a shafinsa na Truth Social inda ya ce yarjejeniyar tana bai wa Amurka damar samun damar shiga kafa sansani da kuma haƙƙin tashi a sararin samaniyar Greenland har abada.

Trump ya ce yarjejeniyar ba ta da wa’adin karewa inda ya kwatanta ta a matsayin “cikar burin Amurka.”

Ya kara da cewa nan ba da jimawa ba Amurka za ta kafa babban karfin soji a tsibirin wanda tuni yake dauke da sansanin Rundunar Sojin Sama da Sararin Samaniya ta Amurka (US Space Force) a arewa maso yammacin Greenland.

KARANTA KUMA: Babu Ja Da Baya Kan Batun Greenland – Shugaba Trump

Wannan yarjejeniya ta sha bamban da kiran da Trump ya yi a baya na cewa Amurka ta mallaki Greenland wadda yanki ce mai cin gashin kanta ta kasar Denmark.

Tuni Amurka ta samu damar tashi a sararin samaniyar Greenland da kuma kafa sansanonin soja a can bisa wata yarjejeniyar tsaro da aka kulla da Denmark a shekarar 1951.

Ofishin Firayim Ministan Denmark ya bayyana cewa yarjejeniyar za ta karfafa tsaro a yankunan Arewacin Tekun Atlantika da kuma yankin Arctic.

Firayim Ministan Greenland Jens-Frederik Nielsen ya ce yarjejeniyar ta yi la’akari da muradun Greenland da kuma matsayinta a fannin hadin gwiwar kasa da kasa.

“Wannan yana amfanar mu duka” in ji shi.

Sai dai ba a bayyana cikakkun bayanai game da yarjejeniyar ba ciki har da ko za a gina sabbin sansanonin sojan Amurka a tsibirin.

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya ce yarjejeniyar ta magance damuwar tsaron Amurka game da Greenland “gaba daya kuma har abada.”

Rubio ya kara da cewa Greenland za ta ci gaba da kasancewa cikin yankin tsaro mai muhimmanci na Arewacin Amurka kuma za a hana abokan gaba shiga yankin da ke kewaye da tsibirin.

Wani jami’in Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ya bayyana cewa, yarjejeniyar ta haramta wa kasashen da ba sa cikin kungiyar NATO gina sansanonin soja a Greenland lamarin da ke bai wa Amurka da kawayenta damar gudanar da wasu muhimman ayyukan zuba jari na musamman wadanda ba a bayyana cikakkun bayanansu ba.

Jami’in ya kara da cewa yarjejeniyar za ta ci gaba da aiki ko da Greenland ta samu ‘yancin kai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button