Afirka

‘Yan Majalisar Dokokin Senegal Sun Yi Watsi Da Muhimmin Kasafin Kudi Lamarin Da Ya Zama Babban Koma-Baya

Majalisar dokokin Senegal da ke da rinjaye a hannun ‘yan adawa a ranar Talata da ta gabata an hana gabatar da gyare-gyare ga kasafin kudin wannan shekarar wanda ke da matukar muhimmanci wajen samun sabon shirin ceto Asusun Ba da Lamuni na Duniya.

Kin amincewa da hakan na tsawaita takaddama kan shirye-shiryen kasafin kudin kasar yayin da hukumomi ke neman sabon shirin samar da kudade.

‘Yan majalisar daga kungiyar Pastef ta Ousmane Sonko wacce ke da rinjaye a Majalisar Dokoki ta Kasa sun yi adawa da daftarin kudirin da kuri’u 109 yayin da 20 suka kaurace. An samu kuri’u uku da suka kaurace.

Majalisar ta riga ta mayar da kudirin ga kwamitin kudi mako guda da ya gabata.

Wannan rashin jituwa zai iya kawo cikas ga fatan Senegal na kada kuri’ar kwamitin IMF kan shirin shekaru uku na dala biliyan 2.2 a farkon wata mai zuwa da nufin daidaita harkokin kudin gwamnati.

Senegal na fama da nauyin bashi wanda Asusun ya ce ya kai kashi 132 cikin 100 na jimillar kayayyakin cikin gida nan da karshen shekarar 2024.

Wannan ya faru ne sakamakon gano biliyoyin daloli a cikin bashin da gwamnatin da ta gabata ta bayar.

Sonko wanda kuma shi ne kakakin Majalisar Dokoki ta Ƙasa yana cikin rikicin siyasa mai ban mamaki da Shugaba Bassirou Diomaye Faye.

Cin zarafin kasafin kuɗi ya zo ne a lokacin da ake fama da tashin hankali a cikin al’umma inda rashin aikin yi ga matasa ya yi yawa da kuma matsalar tsadar rayuwa wanda ya haifar da yajin aikin gama gari na kwanaki uku kwanan nan.

 

 

AP/Aisha.Yahaya, Lagos

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button