Wasanni

Edo Queens Ta Shirya Domin Kare Kambunta Na Gasar NWFL

Kungiyar Edo Queens wacce ke rike da kambun gasar za ta fara kare kambunta ne a karawar da za ta yi da Rivers Angels a ranar 2 ga watan Disamba a wasan bude gasar cin kofin kwallon kafa na mata na Najeriya (NWFL Premiership) na kakar 2026/2027.

Za a buga wasan ne a filin wasa na Samuel Ogbemudia da ke birnin Benin a jihar Edo yayin da sauran wasannin zagaye na farko a dukkan kungiyoyin biyu za su gudana ne a ranar 9 ga watan Disamba 2026.

Edo Queens wadanda suka lashe gasar a kakar 2025/2026 za su kara da tsohuwar abokiyar karawarsu Rivers Angels yayin da dukkan bangarorin biyu ke fatan samun nasara tun da wuri a sabuwar kakar wasan.

A rukunin A Edo Queens za su fafata ne tare da Rangers International Women Rivers Angels Abia Angels Adamawa Queens FC Robo Queens Ahudiyannem Queens da kuma Sunshine Queens.

Rukunin B ya kunshi kungiyoyin Bayelsa Queens Remo Stars Ladies Nasarawa Amazons Delta Queens Heartland Queens Ekiti Queens Pelican Stars da kuma Ibom Angels.

Sauran wasannin rukunin A a ranar Laraba za su hada Rangers International Women da FC Robo Queens Abia Angels za su kara da Ahudiyannem Queens, yayin da Adamawa Queens za su karbi bakuncin Sunshine Queens.

A rukunin B Bayelsa Queens za su karbi bakuncin Nasarawa Amazons Ibom Angels za su fafata da Pelican Stars yayin da Heartland Queens za su kara da Ekiti Queens.

KARANTA KUMA:http://Edo Queens Sun Lashe Kambun Gasar NWFL Premiership

Kalandar gasar ta kuma tanadi lokutan hutawa a tsawon kakar wasan domin bayar da damar gudanar da bukukuwa da sauran ayyuka.

Hutu na lokacin Kirsimeti zai kasance daga ranar 23 ga watan Disamba 2026 zuwa 13 ga watan Janairu 2027 yayin da hutun tsakiyar kakar wasa aka tsara zai gudana daga ranar 28 ga watan Janairu zuwa 3 ga watan Fabrairu 2027. Haka kuma za a samu hutun lokacin Sallah daga ranar 3 ga watan Fabrairu zuwa 17 ga watan Maris 2027.

Ana sa ran wasan bude gasar tsakanin Edo Queens da Rivers Angels zai ja hankali sosai kasancewar masu rike da kambun gasar na fatan fara kare kambunsu da nasara a kan daya daga cikin kungiyoyin da suka dade suna taka rawar gani a kwallon kafa na mata a Najeriya.

Kakar wasa ta 2026/2027 za ta ba wa kungiyoyin da ke shiga gasar wata dama ta sake fafatawa domin lashe babban kofin kwallon kafa na mata na cikin gida a kasar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button