Japan Za Ta Biya Gudummawar ICC Ta Shekarar 2027 Da Wuri Duk Da Takunkuman Amurka

Firayim Minista Sanae Takaichi ta sanar a ranar Talata da ta gabata bayan da kotun ta nemi a ba ta cikakken gudummawar da ta bayar a shekarar 2027 ga Kotun Manyan Laifuka ta Duniya (ICC) kafin karshen wannan shekarar bayan da babbar mai ba da gudummawar kudi ta sanar da cewa za ta dauki matakin gaggawa a kan takunkumin da Amurka ta kakaba mata.
Takaichi ta bayyana wannan matakin ne a lokacin da ta ke gana da shugaban ICC Tomoko Akane a ofishinta a cewar wani rubutu da aka wallafa a asusunta na X.
Wannan matakin ya zo ne yayin da Amurka babbar kawar Japan a fannin tsaro ke kara matsa lamba kan rage karfin kotun ta hanyar sanya takunkumi da kuma matsa lamba ga kasashen mambobinta su janye.
Japan ta bayar da kusan kashi 15 cikin 100 na kasafin kudin ICC wanda hakan ya sanya ta zama babbar mai tallafawa kotun a gaban Jamus Faransa Birtaniya Italiya da Koriya ta Kudu da Kanada.
KARANTA KUMA: Japan Ta Kaddamar da Sabuwar Hukumar Kula da Bala’i
Ana sa ran biyan kudin da wuri zai bai wa kotun damar samun kudi kafin takunkumin Amurka ya fara aiki a watan Afrilun 2027. Masu sharhi sun ce shawarar Japan za ta iya karfafa wa sauran manyan masu bayar da gudummawa gwiwa su biya kafin lokaci wanda hakan zai taimaka wa ICC wajen gina wani katafaren gida na kudi kan tasirin takunkumin.
Reuters/Aisha.Yahaya, Lagos



