Afirka

Sojojin Libya Sun Musanta Samun Sabani Da Masar

Rundunar Sojin Ƙasa ta Libya (LNA) ƙarƙashin jagorancin Field Marshal Khalifa Haftar ta yi watsi da rahotannin da ke nuna cewa dangantaka ta yi tsami tsakaninta da Masar da kuma zargin janye ƙwararrun sojojin Masar daga Benghazi.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, 22 ga Nuwamba ta hannun Ma’aikatar Jagorancin Ɗabi’a LNA ta ce dangantaka da haɗin gwiwa da Alƙahira sun kasance kamar yadda aka saba tana mai sake tabbatar da haɗin gwiwar dabarun da ke tsakanin ɓangarorin biyu.

Rundunar sojin ta bayyana rahotannin da ke yawo a kafafen yaɗa labarai da kuma a shafukan sada zumunta game da tashin hankali tsakanin ƙasashen biyu da kuma janyewar sojojin Masar a matsayin abin da ba shi da tushe.

Ta ce haɗin gwiwa tsakanin Libya da Masar ya wuce batutuwan soja da tsaro har ya haɗa da sake ginawa da ci gaban tattalin arziki.

KARANTA KUMA: Libya Ta Sake Jaddada Goyon Bayanta Ga Kare Yankunan Sudan

Wannan karin haske ya zo ne bayan da Ministan Jiha na Yada Labarai na Masar Diaa Rashwan ya musanta rahotannin da ke cewa kwararrun sojan Masar sun janye daga birnin Benghazi inda ya bayyana cewa rahotannin ba su da tushe ko kadan.

Haka kuma Rashwan ya sake jaddada goyon bayan Masar ga zaman lafiyar Libya da kare yankunanta da kuma dorewar cibiyoyin kasar.

Wadannan kalaman sun zo ne a daidai lokacin da Masar ke kokarin ci gaba da kulla alaka da bangarorin siyasa da na soja masu adawa da juna a Libya wato gwamnatin Abdelhamid Dbeibah da ke Tripoli da kuma bangaren Haftar da ke gabashin kasar.

Masar tana da muhimman abubuwan da take son karewa a gabashin Libya musamman ta fuskar tsaron kan iyaka hadin gwiwar soji, da ayyukan sake gina kasar.

 

 

APA/Ladan Nasidi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button