Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Yaba Wa Shugaban NASFAT Kan Ayyukan Yada Musulunci A Duniya

Shugaba Bola Tinubu ya yaba wa Shugaban Ƙungiyar Nasrul-Lahi-L-Fatih (NASFAT) Alhaji Ayodeji Abdulrauf saboda jajircewarsa na samar da jagoranci na addini ga al’ummomin Musulmi a Najeriya da kuma faɗin duniya.

Shugaban ya yi wannan yabo ne a cikin wani saƙon taya murna da ya yi wa ranar haihuwar Alhaji Abdulrauf a ranar 23 ga Nuwamba inda ya yaba da gudummawar da ya bayar wajen yaɗa addinin Musulunci da kuma haɓaka ɗabi’un addini a wajen iyakokin Najeriya.

A cikin wata sanarwa da Mai Ba shi Shawara Kan Yaɗa Labarai da Dabaru Bayo Onanuga ya fitar Shugaba Tinubu ya bayyana shugaban NASFAT a matsayin fitaccen malamin addinin Musulunci malami kuma mai gudanarwa wanda jagorancinsa ya ƙarfafa ayyukan ci gaban addini da al’umma.

KARANTA KUMA: NASFAT Ta Yi Kira Ga Matasa Da Su Shiga Harkar Noma

Shugaba Tinubu ya yaba da rawar da NASFAT ke takawa wajen haɓaka jituwar addini haɓaka ci gaban al’umma da kuma tallafawa shirye-shiryen ƙarfafa tattalin arziki na Gwamnatin Najeriya a ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abdulrauf.

Ya bi sahun iyalan mai bikin abokan aikinsa da kuma membobin NASFAT a duk duniya wajen yabawa gudunmawar da ya bayar ga al’ummar Musulmi da nasarorin da ya samu a matsayinsa na shugaban al’umma.

Shugaban ya yi wa Alhaji Abdulrauf fatan alheri Allah ya ci gaba da yi masa albarka da kuma shekaru masu yawa na hidima mai ma’ana ga ci gaban addini da al’umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button